Leadership News Hausa:
2025-04-22@21:17:19 GMT

Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna

Published: 22nd, April 2025 GMT

Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna

Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a Minna babban birnin jihar, sakamakon yawaitar hare-hare da kashe-kashen da ake yi a birnin. A cewar gwamnan, an takaita zirga-zirgar babura da masu tuka keke napep a tsakanin karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe.

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Wanke Gonakin Shinkafa Sama Da Hekta 10,000 A Neja Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Tare Da Kwato Makamai A Kano Bago ya bayyana hakan ne a yayin wani muhimmin taron tsaro da masu ruwa da tsaki suka yi da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati, ranar Talata. Ya ce, amma dokar ta kebe cibiyoyi da hukumomin kiwon lafiya. Ya bayyana cewa, sabon matakin na da nufin dakile matsalolin tsaro da ke kara tabarbarewa a babban birnin jihar. Gwamnan ya jaddada cewa, gwamnati ba za ta rungume hannu ba, yayin da masu aikata laifuka ke ci gaba da kai hare-hare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Ya kuma umurci gundumomi, ƙauye, da masu unguwanni da su sanya ido kan duk wadanda ke zaune a yankunan su. Ya kuma yi gargadin cewa, duk gidan da aka samu yana dauke da masu aikata laifuka ko masu safarar miyagun kwayoyi za a ruguza shi. A baya-bayan nan dai garin Minna ya sake samun koma-baya na ‘yan daba, da hare-hare, da kashe-kashe, lamarin da ke janyo firgici da damuwa a tsakanin mazauna garin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yan dava Rashin Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Ambaliya ta kashe mutum 3 ta lalata hekta 10,000 na shinkafa a Neja

An tabbatar da rasuwar mutum uku tare da asarar gonakin shinkafa da faɗinsu ya kai hekta dubu 10 a Jihar Neja a sakamakon mummunar ambaliyar ruwa.

Wannan ibtila’i ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Mikawa, sakamakon sakin ruwa daga Madatsar Ruwa ta Jebba.

Shaidu sun bayyana cewa ambaliyar ta yi ɓarna sosai a gonakin yankin.

Shugaban Ƙungiyar Raya Yankin Kede, Abdulraham Abdulƙadir Kede-Wuya, ya ce gonar shinkafarsa mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda suka salwanta a ambaliyar.

Gobara ta ƙone gidaje sama da 100 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi

Ya ce, “gonata mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda ruwan ambaliyar ya shanye, Sannan akwai sauran masu gonaki. Duk gonakin da bain ya shafa sun kai lokacin girbi. Ba mu san abin da ya da suka saki ruwan a irin wannan lokaci ba tare da sanar da al’umma ba.”

Wani manomi a yankin, Ibrahim Ndako, ya bayyana ambaliyar a matsayin bala’i, yana mai kira ga hukumomi su kawo musu ɗauki.

Ibrahim ya bayyana cewa, “Irin asarar asarar rayuka da maƙudan kuɗaɗe da wahalhalun da manoman rani suka tafka a sakamakon wannan abu, da wuya a iya mayar da shi.”

Ya ce yawancin manoma sun zo yankin ne daga jihohi Kebbi, Sakkwato, Zamfara Kano da Borno, domin yin noman rani a yankin, amma yanzu an jawo musu asarar.

Aminiya ta samu labarin cewa wasu daga cikin manoman sun fara girbi a lokacin da ambaliyar ta auku.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Ibrahim Aufu Hussaini ya ce an samu asarar rayukan ne a lokacin da wani kwalekwale ɗauke da su yake ƙoƙarin tsallake kogi da su bayan ambaliyar.

Ya bayyana cewa hukumar tana ci gaba da bincike domin tantance girman asarar da aka yi a sakamakon ambaliyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 12 a Neja
  • Gwamnan Edo Ya Dakatar da Sarki Saboda Matsalar Tsaro A Yankinsa
  • Motar hatsi ta kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
  • Motar hatsi kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
  • HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato
  • Ambaliya ta kashe mutum 3 ta lalata hekta 10,000 na shinkafa a Neja
  • Fursunoni 9 Sun Tsere Daga Gidan Gyara Hali A Jihar Kwara, An Cafko Guda Daya
  • Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue
  • Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar