Iyalen Surajo Malumfashi na Radio Nigeria Kaduna Yana Gayyatar Jama’a Zuwa Daurin Auren ‘Yar Sa
Published: 22nd, April 2025 GMT
Iyalan Alhaji Surajo Ilyasu Malumfashi (RADIO NIGERIA KADUNA) dana Alhaji Idris Ahmed Accama na farin cikin sanar da bikin aure na ‘ya’yansu, Muhammad Auwal Idris da Zainab Surajo Malumfashi.
Za’a gudanar da bikin auren ranar Asabar, 3 ga Mayu, 2025, a Masallacin Juma’a na Dan Fodio, Dake Anguwan Sunusi, Jihar Kaduna.
Za a daura auren da misalin karfe 11:00 na safe, sannan ana sa ran ci gaba da liyafa kai tsaye bayan kammala daurin auren.
Iyalan suna gayyatar dangi, abokan arziki da duk masu fatan alkhairi su halarta tare da murnar wannan babban biki, wanda ke nuna sabon babi a rayuwar amarya da ango.
Surajo Ilyasu Malumfashi
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara ta ƙone gidaje sama da 100 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno
Wata gobara ta ƙone gidajen wuccin gadi sama da 100 ma ’yan gudun hijira a sansanin ’yan gudun hijira na hukumar ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Monguno ta Jihar Borno.
Shaidu sun ce ba a samu asarar rai ba a gobarar da ta tashi da misalin karfe 10.40 na safe na ranar Alhamis da ta gabata, kuma cikin sauri ta bazu a unguwar, inda ta ƙona kayan abinci, da sauran kadarori masu ɗimbin yawa.
Majiyar da ke sansanin ta bayyana cewar an tura jami’an agaji zuwa wurin domin kula da jama’a da kuma hana sace-sacen kayayyakin jama’a da suka rage, yayin da jami’an kashe gobara tare da mazauna sansanin suka yi bakin ƙoƙarinsu wajen kashe wutar.
Tashin gobarar dai ba shi ne karo na farko ba a wannan sansanin, domin ko da a kwanakin baya ma an samu makamancin hakan, lamarin ya sa jama’a ke zargin akwai sakaci daga wasu mazauna wannan sansanin.
Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — HakeemDon haka suka jadadda buƙatar a riƙa yin hattara don kauce wa ci gaba da faruwar irin haka nan gaba, kasancewar yanayin bazara mai dauke da iska ne ke ƙara ƙaratowa a wannan yanki, wanda hakan kan haifar da barazanar yawaitar tashin gobara a lokacin bazara.