ECOWAS Zata YI Taro A Ghana Don Tattauna Batun Niger, Mali Da Burkina Faso
Published: 22nd, April 2025 GMT
Kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fara taro a kasar Ghana don tattauna al-amura da suka shafi kasashen Niger Burkina Faso da kuma Mali.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa agendar taron nasu na kwanaki biyu, sun hada da huldar kungiyar da kasashen uku, musamman cibiyoyin ECOWAS da suke cikin kasashen, sannan da batun kudaden fito na kashi 0.
Daga karshe kungiyar ta bayyana cewa zata fidda tsarin tattaunawa da kasashen uku daya bayan daya don warware matsalolin da ficewar daga kungiyar suka haddasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Rantsar Da Shugabanin Kungiyar KekeNapep A Kaduna
Kungiyar Masu Babura Uku ta Najeriya, Jihar Kaduna ta Rantsar da Shugabannin Sassa Goma Sha Biyar da Manyan Jami’ansu don Gudanar da Harkokin Kungiyar a Tsawon Shekaru Hudu Masu Zuwa.
Mataimakin Kwamandan Hanya kuma Mataimakin Jami’in Wayar da Kai na Hukumar Kiyaye Haddura ta Tarayya (FRSC), Kaduna, Usman Garba, wanda ya yi magana da manema labarai bayan bikin rantsarwa, ya yaba wa kungiyar, yana mai cewa wannan ci gaba ne mai kyau ga kungiyar.
Ya ce Hukumar Kiyaye Haddura na farin ciki da wannan ci gaba saboda sabon tsarin shugabanci zai taimaka wajen magance matsalolin da suka shafi direbobin babura uku (Keke Napep) da hukumar ke fuskanta a jihar.
A cewarsa, yanzu hukumar za ta yi aiki kafada da kafada da kungiyar wajen horas da mambobinta kan amfani da hanyoyin mota da kuma basu ilimi na musamman lokaci zuwa lokaci domin su san yadda za su yi amfani da hanyoyin jama’a yadda ya kamata.
A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Masu Babura Uku ta Najeriya, Jihar Kaduna, Kwamared Jacob Ayuka, ya bayyana cewa kungiyar na taka muhimmiyar rawa a harkar sufuri ta Najeriya.
Ya bayyana cewa, tare da karfi a matakin tushe da kuma samun karbuwa a kasa baki daya, kungiyar na ci gaba da fafutukar ganin an samu ingantattun dokoki, da karfafa wa mambobinta gwiwa, tare da bada gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Kwamared Ayuka ya kara da cewa kungiyar na aiki a matsayin kungiya mai tsari, ba mai neman riba ba, wacce ke kokarin tallafa wa mambobinta ta hanyar fafutuka, shirye-shiryen jin kai, tallafin aiki, da kuma hadin gwiwa da hukumomin gwamnati da hukumomin sufuri.
An rantsar da shugabannin sassa goma sha biyar da jami’ansu bayan gudanar da zabe, kuma an mikawa kowane shugaban sashi takardar shaida ta nasara.
Daga cikin shugabannin da aka rantsar akwai:
Sashin Wusili – Kwamared James Ibrahim Yakubu;
Unguwan Mu’azu – Kwamared Mustapha Aliyu;
Urban Shelter – Kwamared Shehu Lawal;
Kasuwar Sabo – Kwamared Emmanuel Okiki John;
Rain Oil – Kwamared Jacob Ayuka.
Sauran su ne:
Tashar ‘Yan sanda Tsohuwar – Kwamared Paul Dogo;
Rukunin Narayi Junction – Kwamared Tanimu Mohammed;
Jami’ar KASU – Kwamared Sani Adam;
Kongo, Zaria – Aminu Ibrahima.
Kana kuma:
Jan-Ruwa – Kwamared Patrick A. Sanda;
Hayin Mal Bello – Kwamared Abubakar Ilyasu;
FCE Zaria – Kwamared Isyaka Baba Tanko;
Charity – Kwamared Jatau Ango Manga;
Bakin-Ruwa – Kwamared Mahadi Lawan;
AP Maraban Rido – Kwamared Livinus Solomon.
Mataimakin Kwamandan Hanya kuma Mataimakin Jami’in Wayar da Kai na FRSC Kaduna, Usman Garba, na mika takardar shaida ga daya daga cikin shugabannin sassan a yayin bikin.
A nasa bangaren, shugaban sashin Kasuwar Sabo, Kwamared Emmanuel Okiki John, ya bayyana cewa sashin kasuwa ne mai cike da aiki, wanda ke da korafe-korafe da dama, kuma akwai shirin da aka tanadar don gyara lamura.
Kwamared John ya sha alwashin yin aiki tukuru tare da sauran shugabanni don amfanin da ci gaban mambobin kungiyar.
Cov/ Adamu Yusuf