Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana farin cikisa bisa da shirye-shiryen da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta gudanar ya zuwa yanzu, domin aikin Hajjin shekarar 2025.

Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan da ya jagoranci membobin hukumar ta NAHCON domin gabatar wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bayanai kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2025.

Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ke sa ido kan ayyukan NAHCON, kuma Hukumar ta shaida wa Sanata Kashim Shettima cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba domin fara aikin Hajjin 2025 da jigilar mahajjata zuwa ƙasar Saudiyya daga ranar 9 ga Mayu, 2025.

A nasa jawabin bayan ganawar, Kwamishinan NAHCON mai kula da ayyuka, Prince Anofi Elegushi ya bayyana cewa an riga an kammala shirye-shirye a Makka, Madina da sauran wurare domin gudanar da  aikin Hajji cikin sauki.

Ya ce, “Mun tanadi masaukai a Makka, da Madina da sauran wurare, an kuma shirya su domin tarɓar mahajjatanmu, inda muka  samu isassun gadajen, tare da biyan kuɗin abinci mai kyau kuma isasshe ga dukkan mahajjata. Mun zaɓi ranar 9 ga watan Mayu domin tashin jirgin farko zuwa Madina, muna kuma fatan kammala jigilar zuwa Saudiyya kafin ranar 24 ga watan Mayu, kuma mu fara dawo da mahajjata daga ranar 13 ga Yuni har zuwa 2 ga Yuli.”

A  jawabinsa tun da farko, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bukaci Hukumar da ta tabbatar da cewa kowa yana bakin kokarinsa domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.

“Ya zama wajibi a dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2025. Wannan nauyi ne a kanmu ga ‘yan Najeriya da mahajjata, domin mu tabbatar da aikin Hajji mai inganci.” In ji shi

 

Safiyah Abdulkadir

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Mataimakin Shugaban Ƙasa shirye shirye tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Ma’aikatar Shari’a Yana Halartar Taro A Kasar China

Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran ya isa kasar China domin halartar taron shugabannin ma’aikatun shari’a na kasashen da suke mambobin kungiyar Shangai karo na 20.

Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhsini Eiji wanda shi ne shugaban ma’aikatar shari’a ta jamhuriyar musulunci ta Iran, ya nufi kasar China a yau Litinin domin halartar taron kungiyar Shangai wanda shi ne irinsa karo na 20.

Gabanin barinsa filin saukar jiragen sama na “Mehrabad” Eiji ya bayyana muhimmancin yin aiki a tare a tsakanin ma’aikatun shari’a na kasashen mambobin kungiyar Shanghai sannan ya kara da cewa: ” Taron na shugabannin ma’aikatun shari’a karo na 20 na kungiyar Shangai za a yi shi ne a garin Hangatsho, za kuma mu hatarta ne a karkashin bunkasa diflomasiyya ta fuskar shari’a da kuma fadada alaka ta fuskar doka a karkashin wannan kungiya ta Shangai.

Ita dai wannan kungiyar ta Shangai,mambobinta suna da mutanen da su ne kaso 40% na al’ummar duniya,ana kuma daukarta a matsayin kungiyar yanki mafi girma. Kasashen kungiyar dai suna aiki ne domin bunkasa alakar da take a tsakaninsu a fagagen tattalin arziki, siyasa, tsaro,soja da kuma sharia.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hajjin 2025: Sahun Farko Zai Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki 9 Ga Watan Mayu
  • Gwamna Zulum Ya Ƙaddamar Da Aikin Gina Titi Da Gadar Sama Ta Huɗu A Borno 
  • Za’a Yi Zana’izar Paparoma Francis A Ranar Asabar 26 Ga Watan Afrilu
  • Shettima Ya Gayyaci Shugaban NAHCON Da Mambobin Hukumar Kan Shirye-shiryen Hajjin 2025
  • NAJERIYA A YAU: Mene ne Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?
  • Sin: Matakin Harajin Kwastam Da Amurka Ta Dauka Babakere Ne 
  • Shugaban Ma’aikatar Shari’a Yana Halartar Taro A Kasar China
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Bada Tallafin Kudi Ga Manoman Alkama
  • NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya