Iran ta ce an dage tattaunawar matakin kwararru da Amurka zuwa ranar Asabar
Published: 23rd, April 2025 GMT
Iran ta sanar da dage tattaunawar da aka shirya gudanarwa yau Laraba tsakanin tawagar kwararu ta kasar da kuma na Amurka a kasar Oman a wani bangare na ci gaba da tattaunawar da ake tsakanin kasashen biyu kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana cewa, an dage tattaunawar ta matakin kwararru tsakanin Iran da Amurka kan cikakkun bayanai na fasaha na yiwuwar maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015, wadda aka shirya yi a yau ranar Laraba, zuwa ranar mai zuwa 26 ga watan Afrilu.
Esmaeil Baghaei ya bayyana cewa, za a gudanar da taron a daidai lokacin zagaye na gaba na tattaunawar tsakanin jagororin tawagogin guda biyu.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi da Steve Witkoff, manzon musamman na shugaban Amurka kan harkokin yankin gabas ta tsakiya, sun jagoranci tattaunawar wacce ba ta kai tsaye ba har sau biyu kan shirin nukiliyar Iran da kuma dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran a babban birnin Oman na Muscat da babban birnin Italiya, Roma, a ranakun 12 da 19 ga watan Afrilun nan, a shiga tsakanin Ministan harkokin wajen Omani Badr bin Hamad Al Busaidi ne ya shiga tsakani tattaunawar.
A ranar 26 ga watan Afrilu ne ake sa ran gudanar da zagaye na uku na shawarwarin kai tsaye tsakanin Araghchi da Witkoff a kasar Oman domin tantance sakamakon tarukan da masana suka yi da kuma auna yadda suke kusa da cimma matsaya.
A wani labara kuma, ministan harkokin wajen Iran, Araghchi ya tattauna da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, ta IAEA, jiya Talata
Inda ya yi masa bayani kan sabbin abubuwan da suka faru game da tattaunawar da Amurka, yana mai jaddada kudurin Iran na yin shawarwarin bil hakki.
Shi ma Grossi, ya yaba da matakin da Iran ta dauka, ya kuma bayyana shirin hukumar na bayar da duk wani taimako a cikin wannan tsari, daidai da ayyukanta da ikonta kamar yadda dokar hukumar ta IAEA ta ayyana.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana China Da Rasha A Matsayin Abokai Na Tushe Ga Iran
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban.
A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai kyau cewa Iran suna ci gaba da tuntubar juna tare da su a fagage daban-daban, musamman a yanzu da aka tabo batun tattaunawa da Amurka a fakaice.
Araqchi ya ci gaba da cewa: “Suna bukatar su sanar da abokansu da ke kasar China cikakkun bayanai game da abubuwan da ke faruwa tare da tuntubarsu, kuma sun yi hakan a makon da ya gabata a kasar Rasha.” Inda ahalin yanzu suke kasar China, kuma zai isar da sakon shugaba kasar Iran Mas’ud Pezeshkian, kuma idan Allah ya yarda za su yi tattaunawa mai kyau.