Rohoton Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Ya Tabbatar Da Tafka Manyan Laifukan Cin Zarafin Bil-Adama A Siriya
Published: 23rd, April 2025 GMT
Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula
Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”.
Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris.
Rahoton ya yi nuni da wani tsari na cin zarafi da ake yi wa fararen hula, da suka hada da kashe-kashen gilla, azabtarwa, tilasta yin gudun hijira, da wawure dukiyoyi. Har ila yau, rahoton ya yi nuni da yadda dakarun gwamnati da kungiyoyin masu dauke da makamai suka shiga cikin wadannan laifuka, da kuma dogaro da shaidar iyalan wadanda abin ya shafa na tattara bayanan da aka hana binne mutane da kuma wulakanta fararen hula.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: fararen hula
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen 2027: An soma liƙa fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamnan Bauchi
A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.
An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi.
HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a GombeAminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi.
Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ’yan siyasa biyu — Ya’u Ortega da Talolo — ne suka ba su kwangilar.
Auwal ya ce: “an ba mu kwangilar liƙa fastocin gwamnan a manyan hanyoyi da ke cikin birnin Bauchi.
“Tun wurin ƙarfe 1:00 na dare muka fara wannan aiki kuma muna sa ran kammalawa a yau [Litinin].”
Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin ’yan siyasar biyu da suka ba da wannan kwangilar ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.