Yawan Falasdinawan Da Suka Yi Shahada Sakamakon Hare-Haren ‘Yan Sahayoniyya Sun Kai 51,266
Published: 23rd, April 2025 GMT
Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban.
An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga Oktoban shekara ta 2023.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Yi Mummunar Arangama Da ‘Yan Bindiga A Sakkwoto
Mutum ɗaya ya rasu yayin da matasan gari suka yi taho mu gama da ‘yan bindiga lokacin kai hari garin Kware a Jihar Sokoto a daren Asabar. Shaidu sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin Kware, cibiyar ƙaramar hukumar Kware, da nufin aikata fashi.
Mamba na ƙungiyar masu samar da tsaro ta cikin gari, Bello Mai Maciji, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun samu nasarar satar wani adadin kudi daga hannun Dan Balgore, wani sanannen mai kasuwanci a yankin.
Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100 ‘Yan Bindiga A Ƙarƙashin Jagorancin Turji Sun Kashe Manoma 12 A SokotoMai Maciji ya bayyana cewa, ‘yan fashin sun bayyana cewa suna da masaniya game da kuɗin kasuwancin da yake ɗauke da shi a cikin motarsa, lokacin da suka kai harin yayin da Balgore ya tsaya a cikin garin don sayen abinci. Mai Maciji ya ƙara da cewa, mutumin da ya mutu ya rasu ne bayan ya ji raunukan harbi yayin harin.
Duk da haka, Mai Maciji ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun gudu lokacin da matasan gari suka afka musu. Sun kona wani shago a kasuwar, amma wutar ba ta bazu zuwa sauran shaguna ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp