Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu

Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza,  yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.

Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa ta hanyar kai hare-hare wuce gona da iri kan wuraren dafa abinci da wuraren jin dadin jama’a, wadanda ke ba da taimako kadan ga matalauta da mabukata. Ya yi kira da a gaggauta bude mashigar kai daukin gaggawa zuwa Gaza, tare da ba da izinin gabatar da agajin jin kai, irin abinci, da magunguna cikin Gaza ba tare da wani bata lokaci ko sharadi ba, don ceton rayukan mutane da dama.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu na yau za yi magana dangane da “Rage kisasfin kudan ma’aikatar harkokin wajen Amurla da kimani kasha 50% da kuma tasirinsa ga matsayin Amurka a duniya da kuma cikin gida. Wanda ni tahir amin zan karanta.

A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan, rahe kasafin kudi na ma’aikatar harkokin wajen kasar da kasha 50%, saboda haka kuma ya rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancin kasar da kananan ofisoshin jakadancin kasar fiye da 30 a yankuna daban daban a duniya amma mafi yawansu a nahiyar Afirka.

Dangane da wannan matakin da gwamnatin kasar Amurka masana daga ciki ga wajen kasar ta Amurka masu yawa sun nuna damuwarsu da kuma rashin amincewarsu da hakan.

A majalisar dokokin kasar, wakilai daga jam’iyyu biyu masu mulkin Amurka wato Republican da kuma Democrat sun nuna rashin amincewarsu da matakan da shugaba Trump ya dauka, suna kuma ganin hakan wata alama ce jada bayan Amurka daga harkokin kasashen duniya, kuma da haka tauraron kasar zata dushe a duniya. Sannan akwai has ashen cewa kasar China zata maye gurbin Amurka a cikin al-amura da dama, musamman a kasashen da Amurka ta janye.

Kafin haka dai shugaban kasar Amurka ya janye kasar Amurka daga manya-manayn kungiyoyin bada agaji a duniya, wadanda suka hada da hukumar lafiya ta duniya WHO, hukumar abinci ta duniya.

Banda haka Amurka ta janye tallafin da take bawa kungiyar tsaro ta NATO wanda yake taimakawa abokan kasar na turai kan abubuwan da suka shafi tsaro, da kuma wasu al-amur da dama.

Masu sukan shugaban daga cikin har da sanatoci da tsoffin janar-janar na sojojin Amurla wadanda suka yi ritaya kimani 120 suke ganin, shugaban trump ya mikawa kasashen China da rasha dukkan wuraren da ya janye tallafi, ko kuma ya rufe ofishin jakadancin Amurka a duniya.

Wadannan masana dai suna ganin, ragewa ma’aikatar harkokin wajen kasar kudede masu yawa wanda ya kai dalar biliyon kimani 25, ya nuna cewa gwamnatin Amurka bata da wakilai a wasu wurare masu mihimmanci da dama a duniya, don haka ba zata sami labarin abinda yake faruwa a cikinsu ba. Kuma mai yuwa samun wadannan labarai suna da muhimmanci.

Wasu masu sukan suna ganin a halin da ake ciki mafi yawan kawayen Amurka, musamman kasashen turai sun tashi daga abokan aiki zuwa ga makiya ga gwamnatin Amurka. Sannan a kasashen masu tasowa, wadanda suke neman tallafi da taimako, Amurka ta bawa kasar China da Rasha dama ta su amfana da wadannan kasashe, ko basu bada kyauta ba, amma suna iya zuba jari a cikin kasashen inda bangarorin biyu zasu amfana.

A wani bangare kuma shugaban yana da shirin rage kudaden da ake kashewa ayyukan gwamnati a cikin gida, inda hakan ya kai ga rufe kafafen yada labarai da daman a gwamnatin Amurka. Hakan ya sa mutane da dama sun rasa ayyukansu a cikin kasar. Sannan daga kasashen waje ba, dubban ma’aikata sun rasa ayyukan daga kungiyoyin bada agaji ko kiwon lafiya ko tallafawa yara karkashin MDD wadanda gwamnatin Trump ta janye tallafin da suke bayarwa.

Daga karshe masana suna ganin, idan wannan halin ya ci gaba da alamun shugaba Donal Trump kama hanyar rusa kasar Amurka daga ciki da kuma wajen kasar a cikin shekaru 4 da zai yi a matsayin shugaban kasa. Mai yuwa gwamnatin da zata zo bayan tasa ta gaggauta gyaran wasu daga cikin abubuwan da ya bata. Amma wasu barnan da yayi ba zasu sake gyaruwa ba.

Don haka daga karshen dai Amurka ta kama hanyar wargajewa, idan ba an yi wani abu da gaggawa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila
  • Kungiyar kare farar hula ta Falasdinu ta zargi sojojin da ” kashe-kashe masu yawa”
  • Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa
  • A Kalla Falasdinawa 35 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24
  • Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Amnesty International Ta Ce; Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ba Ta Dace Da Bincike Laifukan Sojojinta Ba
  • Wasu Falasdinawa Sun Yi Shahada A Harin Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Zirin Gaza
  • Boko Haram Na Yin TikTok, Suna Sarrafa Jirage Marasa Matuƙi Don Sa Ido Kan Sansanonin Soji – Bulama 
  • Gaza : Red Crescent ta yi watsi da rahoton Isra’ila kan kisan da aka yi wa jami’an agaji
  • Bikin Easter : Paparoma Francis ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza