Aminiya:
2025-04-23@22:20:39 GMT

Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro

Published: 23rd, April 2025 GMT

Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki.

 Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Ibadan da ke Oyo mai dauke da sa hannun shugabanta, Adebo Ogundoyin.

Ya bayyana cewa kashe-kashen dubunnan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba ya janyo musu asarar gidajensu, da dukiyoyinsu, yana haifar musu da tashin hankali.

“Mun kaɗu ƙwarai da yadda matsalar tsaro ke ƙara ƙamari a Nijeriya, da kuma rashin tabbas da ke biyo bayan kashe-kashen.

“Lokacin yin Allah-wadai ya wuce, yanzu matakin gaggawa ya dace gwamnatocin dukkanin matakai su ɗauka domin kawo karshen masifar nan.

“Mun san cewa tsaron kasa na hannun gwamnatin Tarayya ne, amma mu sani gwamnatin kowanne mataki na da alhakin tsaro da walwalar jama’arta, musamman gwamnonin jihohi.

“Bai dace aikinku ya tsaya a yin tituna da tarukan bukukuwa ba. Gwamnatin gaskiya ita ce wacce ta kafu akan kare rayukan al’umma, tabbatar da doka da oda, da kuma raba su da wahala.” In ji shi.

Daga nan ya yi kira ga gwamnatocin jihohin da su taimaka wa yunƙurin gwamnatin tarayya a ɓangaren tsaro ta hanyar samarwa da tilasta bin dokoki da sauran tsare-tsare a matakin unguwanni.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Binuwai Kwara matsalar tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 12 a Neja

Gwamna Umar Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 12 a birnin Minna na Jihar Neja.

Wannan dai na zuwa ne sakamakon hare-haren da ya janyo salwantar rayuka da aka samu a bayan nan a babban birnin.

Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana HOTUNA: Yadda Pantami ya kai wa Sheikh Jingir ziyarar ta’aziyya

A cewar gwamnan, an haramta zirga-zirgar baburan ’yan acaɓa da masu Keke Napep daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safiyar kowacce rana.

Gwamnan ya bayyana hakan a yayin wani taro na musamman da ya gudana da masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da ya ƙunshi sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a Fadar Gwamnatin jihar a ranar Talata.

A yayin da dokar ba ta shafi duk wata buƙatar lafiya ta gaggawa, Bago ya ce ba a buƙatar ganin ababen hawa daga lokacin da dokar ta fara aiki da zummar daƙile matsalar tsaro da babban birnin ke fuskanta.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zuba ido a yayin da miyagu ke ci gaba da kai hare-hare da kashe mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Ya umarci dukkan dagatai da masu unguwanni da su tabbatar da ɗaukar bayanan duk wasu baƙi da suka shigo yankunansu.

Kazalika, ya yi gargaɗin cewa duk gidan da aka kama yana bai wa miyagu mafaka ko masu fataucin muggan ƙwayoyi za a rushe shi.

A ’yan kwanakin nan dai birnin Minna na fuskantar matsalar tsaro da ta haɗa da dabanci, hare-hare da kisan kai da sauran miyagun ababe masu ɗaga hankalin mazauna.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya gana da shugabannin tsaro a Abuja
  • Rashin Tsaro: Tinubu Ya Gana Da Shugaban Tsaro Da Ribadu Kan Kashe-kashen Rayuka
  • Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya
  • Sabuwar Ƙungiyar ‘Yan Bindiga Ta Addabi Jihohin Kwara Da Neja
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna
  • An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 12 a Neja
  • Gwamnan Edo Ya Dakatar da Sarki Saboda Matsalar Tsaro A Yankinsa
  • HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato
  • Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Amnesty International Ta Ce; Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ba Ta Dace Da Bincike Laifukan Sojojinta Ba