WHO: Masu Ciwon Koda 400 A Gaza Sun Mutu Saboda Rashin Magani
Published: 23rd, April 2025 GMT
Hukumar lafiya ta duniya (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar.
Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a cikin asibitoci.
Ita ma hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa; masu fama da cutar koda a yankin suna fama da matsaloli na rashin Magani, kuma daruruwa daga cikinsu sun mutu saboda hakan.
Haka nan kuma ta yi ishara da yadda mutane 400 daga cikinsu su ka rasu, da hakan yake nufin kaso 40% na adadin masu wannan cutar.
A gefe daya, ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinu ta yi tir da yadda ‘yan mamaya su ka kai wa asibitin “Durrah” na yara hari a gabashin birnin Gaza.
Haka nan kuma hukumar kiwon lafiyar ta Gaza, ta tabbatar da cewa hare-haren da ‘yan mamayar su ka kai wa dakin da yake kula da marasa lafiya na musamman a cikin asibitin kananan yaran, da kuma tashar samar da wutar lantarki a cikin asibitin.
Sanarwar hukumar lafiya ta Gaza ta ce, baya ga hana shigar da abinci da magani da ‘yan mamayar suke yi, suna kuma hana Falasdinawa ci gaba da rayuwa. Ita kuwa hukumar agaji ta “Red-Crecent” ta bayyana cewa; ‘Yan mamaya sun tafka laifukan yaki da su ka hada da kashe masu aikin agaji a cikin watan Maris.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hukumar lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Motar hatsi ta kashe masu bikin Ista 5 a Gombe
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe.
Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista.
An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a BauchiA wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti.
Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin, wasu fusatattun matasa sun cinna wa motar wuta tare da sace kayayyakin da ta ɗauko.
“Lokacin da ‘yan sanda suka kai ɗauki, matasan sun yi musu ruwan duwatsu, sai dai an shawo kan lamarin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.”
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Gombe, Bello Yahaya, ya bayyana jimami kan faruwar lamarin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan.
Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana damuwa kan wannan iftila’i.
A cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai na gidan gwamnati, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa lamarin abu ne mai girgiza zuciya.
Gwamnatin jihar ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin magani ga waɗanda suka ji raunuka, tare da tabbatar da cewa za a ɗauki matakan kare faruwar irin wannan matsala a nan gaba.