Tinubu ya gana da shugabannin tsaro a Abuja
Published: 24th, April 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya gana da babban mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, da hafsan hafsoshin tsaro na ƙasa, Christopher Musa.
Rahotanni dai na nuna sun shiga taron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 3 na rana.
Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APCWannan dai shi ne karo na farko da Tinubun ke ganawa da jagororin tsaron tun bayan dawowarsa daga Faransa da Birtaniya ranar Litinin.
Kafin dawowarsa dai, ‘yan siyasa da dama da sauran al’umma sun koka ka yadda shugaban ya shafe sati biyu a ƙasashen duk da cewa matsalar tsaro na ci gaba da tabarbarewa a tasa ƙasar.
Sai dai babu tabbacin cewa taron da shugabannin suka gudanar na da alaƙa da rikice-rikicen ko akasin haka.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato
Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Filato ta gudanar da wata zanga-zangar lumana domin nuna adawa da matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Zanga-zangar ta gudana ne makonni kaɗan bayan munanan hare-haren da aka kai a wasu ƙauyukan Bokkos da Mangu, waɗanda suka yi sanadiyyar aƙalla rayuka 100.
Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma FrancisWaɗanda suka yi zanga-zangar sun haɗa da maza da mata da matasa har da tsofaffi ɗauke da alluna waɗanda aka rubuta wa saƙonni daban-daban.
Bayanai sun ce maƙasudin zanga-zangar ita ce kiran gwamnati kan ta ɗauki mataki kan kashe-kashen da ake yi a yankin.
Jihar Filato da wasu jihohin Arewa maso tsakiyar Nijeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro duk da matakan da hukumomi ke cewa suna ɗauka domin kawar da matsalar.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma rikice-rikice masu alaƙa da bambancin addini da na ƙabila sun haifar da rasa rayukan ɗaruruwan mutane da tarwatsa wasu daga matsugunansu.
A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Filaton, Caleb Manasseh Mutfwang ya sanar da ɗaukan wasu sabbin matakai na daƙile matsalar, ciki har da hana kiwon dare da kuma farfaɗo da ƙungiyoyin ’yan sintiri na sa-kai.