Shawarar Tabbatar Da Tsaro A Duniya Ta Samar Da “Kyakkyawan Fata” Ga Duniya Mai Fama Da Tashin Hankali
Published: 24th, April 2025 GMT
Na uku, ba da ra’ayin samun tsaro kafada da kafada, inda aka jaddada cewa, ya dace kasa da kasa su yi fatali da ra’ayin nuna wa juna fito-na-fito, kana, su fuskanci dimbin kalubalen tsaro cikin hadin-gwiwa.
Na hudu wato na karshe, tallata ra’ayin tabbatar da tsaro mai dorewa, wato a maida hankali kan dorewar tsaro na wani dogon lokaci.
Wannan shawarar tsaron da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ta samu amincewa sosai daga mutanen kasa da kasa, inda ya zuwa yanzu, ta riga ta samu goyon-baya daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 120, kana kuma, an rubuta shawarar cikin takardun hadin-gwiwa sama da 120 game da mu’amalar kasar Sin da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa.
Shawarar ta kuma shaida cewa, tsaro ba harka ce ta wata kasa ita kadai ba, harka ce da ke bukatar tafiya gaba cikin hadin-gwiwa. Kana kuma ko wace kasa za ta iya cin alfanu daga ciki. Kamar yadda masharhantan kasa da kasa suka bayyana, shawarar nan ta samar wa duniyarmu da ke fama da rikice-rikice wani abun da take matukar bukata, wato “kyakkyawan fata”. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Sami Lambobin Yabo 8 A Wasan Taekwondo Na Duniya
Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa.
An fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa.
Daga cikin lambobin yabon din da tawagar ta Iran ta lashe da akwai gwala-gwalai 4, azurfa 3 da kuma tagulla.