Sin Ta Ce Ya Kamata Amurka Ta Tattauna Da Ita Bisa Mutuntawa Matukar Da Gaske Take
Published: 24th, April 2025 GMT
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son gwabza yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, amma kuma ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba idan yakin ya kaure, yana mai nuni da cewa, idan har Amurka ta zabi fafata yakin kasuwanci, Sin za ta sha damarar yakin har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi.
Bugu da kari, dangane da batun yadda a baya-bayan nan kafafen yada labarun kasar Panama suka soki Amurka kan yin katsalandan da nuna babakere a kasashen yankin tsakiyar Amurka, musamman a kasar ta Panama, inda suka zargi Amurkar da yunkurin karbe ragamar mashigin ruwan Panama ta hanyar fakewa da wai “barazanar kasar Sin” wadda babu ita kwata-kwata. Guo Jiakun ya mayar da martani inda ya ce, bayanan da kafafen yada labarai na Panama suka yi sun fallasa ainihin halin Amurka na babakere.
Guo ya kara da cewa “Babu wata karya da za ta iya lullube ungulu da kan zabon Amurka a kan burinta na neman karbe akalar mashigin ruwan Panama”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Darajar Cinikin Sarin Kaya Da Sayen Kayan Masarufin Sin Ta Karu Da Dala Biliyan 452.5 a Rubu’In Farkon Bana
Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a rubu’in farko wato daga watan Janairu zuwa Maris na bana, darajar wadannan bangarori ta karu da dalar biliyan 452.5 a wadannan watanni uku, wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na makamancin lokacin bara, kana adadin ya kai kashi 10.4% bisa na dukkan GDPn kasar.
Nagartacciyar bunkasar wadannan sana’o’i na nuna goyon baya na tsarin habaka bukatu cikin gidan kasar da tafiyar da tattalin arzikin al’umma ba tare da tangarda ba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp