Iran za ta karbi bakuncin taron farko kan kare hakkin dan Adam a Gabas ta tsakiya
Published: 24th, April 2025 GMT
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, za ta karbi bakuncin taron farko na kasa da kasa kan kare hakkin bil adama a Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Hukumar Al’adu da Sadarwa ta Musulunci Mohammad Mehdi Imanipour ya bayyana cewa, za a gudanar da taron farko na kasa da kasa kan batun kare hakkin bil’adama kan Gabas ta Tsakiya a lokaci guda a Tehran, Qom da Isfahan daga ranar 28 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu.
Hakkin dan adam na daya daga cikin batutuwan da suka fi muhimmanci a cikin al’ummomi, saidai a baya bayan nan wasu gwamnatoci sun yi watsi da yancin dan adam gaba daya.
Mohammad Mehdi Imanipour ya ce “A yau, misali karara na take hakkin bil’adama shi ne kisan kiyashi da ake yi a Gaza.”
Ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da abubuwa da dama da za ta iya fada a fagen kare hakkin bil’adama, don haka ta kai ga gayyatar wasu kasashe a wannan taro domin neman kafa kawancen kare hakkin bil’adama na duniya mai sabon salo.
An aika gayyata a hukumance ga kasashem duniya 32 da kuma manyan cibiyoyin kimiyya da ilimi 36 dake hadin gwiwa tare da taron.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kare hakkin bil adama
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: Yake-yaken Haraji Da Kasuwanci Na Tauye Hakkoki Da Muradun Dukkan Kasashe
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya.
Yayin ganawarsa da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev, shugaba Xi ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana da muradin yin hadin gwiwa tare da kasar Azabaijan wajen kiyaye tsarin kasa da kasa a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa dokokin da aka amince da su a duniya, da yin tsayuwar daka wajen kare halastattun hakkoki da muradu, da kare daidaito da adalci na kasa da kasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp