Jiragen yakin Amurka sun kara kai hari kan kasar Yemen
Published: 24th, April 2025 GMT
Amurka ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a Yaman, a daidai lokacin da kasar Larabawar ke ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza.
Gwamnonin Sana’a da Sa’ada su ne wuraren da Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare a safiyar Alhamis.
A birnin San’a, jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare 6 a yankin Barash da ke gabashin Dutsen Nuqum.
Har ila yau Amurka ta kai hari a unguwar Al-Jarf da ke gabashin gundumar Sha’ub ta lardin Sana’a.
A arewa maso yammacin kasar, an kai wasu hare-hare 6 ta jiragen yakin Amurka a yankin Sahlin da ke gundumar Al Salem a gundumar Sa’ada.
Har ila yau, Amurka ta kai wasu jerin hare-hare ta sama kan lardin Al-Hudaidah, inda ta kai hari a gundumar At-Tuhayta da wasu hare-hare.
Kawo yanzu dai babu wani rahoto kan samun hasarar rayuka ko jikkata.
Harin na Amurka ya zo ne sa’o’i bayan da Yemen ta kai wani muhimmin hari kan Isra’ila a Haifa, ta hanyar amfani da makami mai linzami.
Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana a jiya Laraba cewa, dakarun Yemen sun harba makami mai linzami a wani hari a birnin Haifa da ke arewacin yankunan da aka mamaye.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet.
An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow.
Shugabanni daga kasashe da hukumomin duniya sama da 20 ne aka gayyata domin halartar bukukuwan. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp