Iran ta jinjinawa Sin da Rasha a matsayin kawayenta na kut-da-kut
Published: 24th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing domin yin shawarwari da manyan jami’an kasar Sin, gabanin yin tattaunawa zagaye ta uku da Amurka kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Abbas Araghchi ya shaida wa kafar yada labaran Iran a babban birnin kasar Sin a ranar Laraba cewa, “Sin da Rasha abokan hulda ne na kut da kut da suka tsaya tare da mu a lokutan wahala, don yana da kyau da ma’ana mu ci gaba da tuntubar juna tare da su a bangarori daban-daban, musamman ma yanzu da ake tattaunawa da Amurka.
“Ya zama dole mu sanar da abokanmu a kasar Sin cikakken bayani game da al’amuran da ke gudana tare da tuntubarsu.” Inji shi.
Yayin da yake jaddada cewa, ya yi irin wannan ganawa da manyan jami’an kasar Rasha a birnin Moscow a makon jiya, Araghchi ya ce yana fatan samun kyakkyawar tattaunawa da mahukuntan Beijing, domin isar da sakon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ga mahukuntan kasar Sin.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce, “A baya kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kuma mai ma’ana a batun nukiliyar kasar Iran, kuma ko shakka ana bukatar hakan.
Za mu ci gaba da tuntubar Sin a matsayinta na mamba a kwamitin sulhun MDD, mamba a kwamitin gudanarwar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, bugu da kari kawa ta kut-da-kut ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inji ministan harkokin wajen kasar ta Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta jaddada cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Gudanar Da Tattaunawa Kan Tsaronta Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Iran ba za ta taba gudanar da shawarwari kan tsaronta ba
A cikin jawabinsa na shirye-shiryen shirin zaman taron Carnegie kan manufofin nukiliya na kasa da kasa da aka soke a yanzu, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa kamfanonin Amurka za su iya cin gajiyar damar dala tiriliyan da tattalin arzikin Iran ke samarwa kuma kasuwar Iran za ta iya farfado da masana’antar nukiliyar Amurka da ta tsaya cak.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin shawarwari da tattaunawa a fili a bainar jama’a.”
Araqchi ya ci gaba da cewa, “A cikin jawabinsa, ya kuma bayyana karara cewa wasu ‘kungiyoyin masu sha’awa na musamman’ na kokarin yin magudi tare da bata tsarin diflomasiyya ta hanyar bata sunan masu tattaunawan tare da yin kira ga gwamnatin Amurka da ta gabatar da bukatu mafi tsanani da girma.”