Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji
Published: 24th, April 2025 GMT
Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya ba wa dakarun rundunar wa’adin wata guda su fatattaki sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta Mahmud a da ta ɓulla a Jihar Kwara.
Oluyede ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake jawabi ga sojojin a ziyarar da ya kai Barikin Sobi da ke Ilorin, babban birnin jihar.
“Daga wata mai zuwa, ba na son in ƙara jin mostin waɗannan ’yan ta’addan a yankin Dam ɗin Kainji,” in ji babban hafsan sojin.
Ya umarce su da su kawar da ’yan ta’addan daga ƙananan hukumomi biyun da suka addaba, yana mai jaddada cewa yana son a kammala aikin cikin wata mai zuwa.
Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa gidan rediyo na haɗin gwiwa NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka KasuwanciBabban hafsan sojin ya ce Najeriya ba za ta iya ba da damar ’yan fashin daji ko ’yan ta’adda su ƙara yaɗuwa zuwa wani ɓangare na ƙasar ba.
“Don haka, kuna nan kuma na san za ku yi hakan don tabbatar da cewa waɗancan mutanen sun bar mana wannan wurin,” kamar yadda ya shaida wa sojojin.
“Idan suna son shiga wata ƙasa, wannan su ta shafa, amma dole ne ku kawar da su daga waɗannan dazuzzukan don kada mu sake samun wata ƙungiyar Boko Haram da za ta dame mu a nan.
“Ina iya gaya muku, cikin wata mai zuwa, al’amura za su bambanta. Abin da ke faruwa a Kwara ba zai iya yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya gaba ɗaya ba; lamari ne keɓantacce kuma za mu magance shi kai tsaye.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Aljeriya ta yi gagarimar korar bakin haure a rana guda zuwa Nijar
Aljeriya sun kori fiye da bakin haure 1,100 zuwa Nijar a rana guda, al’amarin da ba a taba ganin irinsa ba.
Bakin hauren da hukumomin Aljeriyar suka bayyana da basa bisa ka’ida, an kora su a cikin hamadar sahara a ranar Asabar din da ta gabata, Inda sukayi tattaki zuwa kan iyakar kasar Nijar, kasar da dubban bakin haure ke bi domin zuwa Libya da Aljeriya domin isa Turai.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka kori bakin haure da dama daga kasar Aljeriya a lokaci guda.
A cewar kungiyar ‘Alarme Phone Sahara’ ta Nijar da ke taimakawa bakin haure a cikin hamada, an kori mutane 1,140 a lokaci guda, adadin da ba a taba ganin irinsa ba.
Galibin bakin hauren sun fito ne daga kasashen kudu da hamadar Sahara, uku kuma sun fito ne daga kasar Bangladesh.
A shekarar 2024, an kori fiye da mutane 30,000 daga Aljeriya.