Aminiya:
2025-04-24@12:25:43 GMT

Sakataren PDP: Damagum ya amince da matsayar gwamnoni

Published: 24th, April 2025 GMT

Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa.

Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas za su zaɓi cikakken sakatare wanda Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar zai amince da shi.

Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke kan wanda ya cancanci ya riƙe muƙamin tsakanin Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, ta ba jam’iyyar ikon yanke shawara kan shugabanninta.

Sai dai a wata takarda da Alhaji Gurama Bawa, jami’in gudanarwa na mukaddashin shugaban jam’iyyar ya fitar, ta ce Setonji Koshoedo, Mataimakin Sakatare na Ƙasa (DNS), yanzu shi ne Mukaddashin Sakatare na Ƙasa na babbar Jam’iyyarmu har sai an sanar da wani abu.

Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci

Takardar ta kuma roƙi ma’aikatan jam’iyyar da su ba sabon mukaddashin sakataren goyon baya wajen gudanar da ayyukansa.

Takardar ta ce: “Dangane da abin da ke sama, duk wasiƙun jam’iyyar ya kamata a tura su ga Hon. (Arch) Setonji Koshoedo.

“An roƙe ku da ku ba shi duk goyon baya da haɗin kai da ys dace a matsayinsa na Mukaddashin Sakatare na Ƙasa na babbar Jam’iyyarmu.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: sakataren jam iya

এছাড়াও পড়ুন:

Hajjin 2025: Kashim Shettima Ya Jinjinawa Hukumar Alhazai Bisa Matakan Da Ta Dauka

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana farin cikisa bisa da shirye-shiryen da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta gudanar ya zuwa yanzu, domin aikin Hajjin shekarar 2025.

Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan da ya jagoranci membobin hukumar ta NAHCON domin gabatar wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bayanai kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2025.

Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ke sa ido kan ayyukan NAHCON, kuma Hukumar ta shaida wa Sanata Kashim Shettima cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba domin fara aikin Hajjin 2025 da jigilar mahajjata zuwa ƙasar Saudiyya daga ranar 9 ga Mayu, 2025.

A nasa jawabin bayan ganawar, Kwamishinan NAHCON mai kula da ayyuka, Prince Anofi Elegushi ya bayyana cewa an riga an kammala shirye-shirye a Makka, Madina da sauran wurare domin gudanar da  aikin Hajji cikin sauki.

Ya ce, “Mun tanadi masaukai a Makka, da Madina da sauran wurare, an kuma shirya su domin tarɓar mahajjatanmu, inda muka  samu isassun gadajen, tare da biyan kuɗin abinci mai kyau kuma isasshe ga dukkan mahajjata. Mun zaɓi ranar 9 ga watan Mayu domin tashin jirgin farko zuwa Madina, muna kuma fatan kammala jigilar zuwa Saudiyya kafin ranar 24 ga watan Mayu, kuma mu fara dawo da mahajjata daga ranar 13 ga Yuni har zuwa 2 ga Yuli.”

A  jawabinsa tun da farko, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bukaci Hukumar da ta tabbatar da cewa kowa yana bakin kokarinsa domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.

“Ya zama wajibi a dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2025. Wannan nauyi ne a kanmu ga ‘yan Najeriya da mahajjata, domin mu tabbatar da aikin Hajji mai inganci.” In ji shi

 

Safiyah Abdulkadir

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tallafa Wa Al’umma: Ya Dace Gwamnoni Su Yi Koyi Da Jihar Zamfara – UNDP
  • Ya isa haka: Tinubu ya umarci shugabannin tsaro su kawo ƙarshen kashe-kashe
  • Tinubu ya gana da shugabannin tsaro a Abuja
  • Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC
  • Hajjin 2025: Kashim Shettima Ya Jinjinawa Hukumar Alhazai Bisa Matakan Da Ta Dauka
  • Ganduje Ya Soki Buba Galadima, Ya Ce “Ɗan Siyasa Ne Mara Tasiri”
  • 2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasa Na Gwamnan Bauchi Sun Bayyana
  • NAJERIYA A YAU: Mene ne Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?
  • Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai