Shi dai filin jirgin saman, wanda gwamnatin Umaru Bago ta gina a Jihar Neja, an raɗa masa sunan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

 

Jirgin kasuwancin na farko mallakin kamfanin Overland Air mai lamba 5N-CCN ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana.

 

Cikin fasinjojin akwai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, Minista Mohammed Idris, tsohon Gwamnan Neja Dakta Babangida Aliyu, Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, da wasu manyan jami’an gwamnati.

 

Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda samar da yanayin da ya bai wa filin jirgin damar fara aiki, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen inganta ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.

 

Haka kuma, Ministan ya jinjina wa Gwamna Bago bisa hangen nesa da jajircewar sa na buɗe Jihar Neja ga cigaban noma da kasuwanci da masana’antu da kuma inganta tattalin arzikin jihar.

 

Ya ce: “Dole ne mu yaba wa shugaban ƙasar mu kamar yadda gwamnan mu ya faɗa. Wannan haƙiƙa mafarki ne da ya zama gaskiya. Gwamnan ne ya sa hakan ya tabbata. Yana da kwaɗayin ganin Jihar Neja ta buɗe ƙofar cigaba ta fannin noma, kasuwanci, masana’antu da kuma bunƙasar tattalin arziki.”

 

A nasa jawabin, Gwamna Bago ya ce wannan jirgi na farko wani ɓangare ne na buɗe jihar zuwa ga duniya baki ɗaya.

 

Ya ce: “Shugabannin kamfanin Overland sun nuna karamci matuƙa wajen ba mu wannan sabon jirgi daga Legas zuwa Minna, sannan yanzu daga Minna zuwa Abuja, kuma hakan zai riƙa faruwa sau uku a mako – a ranakun Litinin, Laraba da Juma’a. Wannan jirgi ne na buɗe hanya – buɗe Jihar Neja ga sararin samaniyar duniya.

 

“Muna son gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda filin jirgin ya samu suna daga gare shi, saboda ya ba mu dukkan goyon bayan da muke buƙata.”

 

Gwamna Bago ya ƙara da cewa jihar tana da niyyar amfani da filin jirgin wajen fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje don haɓaka tattalin arzikin jihar da zama ɗaya daga cikin manyan masu fitar da kayan noma daga Nijeriya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Aljeriya ta yi gagarimar korar bakin haure a rana guda zuwa Nijar

Aljeriya sun kori fiye da bakin haure 1,100 zuwa Nijar a rana guda, al’amarin da ba a taba ganin irinsa ba.

Bakin hauren da hukumomin Aljeriyar suka bayyana da basa bisa ka’ida, an kora su a cikin hamadar sahara a ranar Asabar din da ta gabata, Inda sukayi tattaki zuwa kan iyakar kasar Nijar, kasar da dubban bakin haure ke bi domin zuwa Libya da Aljeriya domin isa Turai.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka kori bakin haure da dama daga kasar Aljeriya a lokaci guda.

A cewar kungiyar ‘Alarme Phone Sahara’ ta Nijar da ke taimakawa bakin haure a cikin hamada, an kori mutane 1,140 a lokaci guda, adadin da ba a taba ganin irinsa ba.

Galibin bakin hauren sun fito ne daga kasashen kudu da hamadar Sahara, uku kuma sun fito ne daga kasar Bangladesh.

A shekarar 2024, an kori fiye da mutane 30,000 daga Aljeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bayyana Filin Jirgin Sama Minna a Matsayin Mafita Ga Jiragen da ke sauka Abuja
  • Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji
  • Aljeriya ta yi gagarimar korar bakin haure a rana guda zuwa Nijar
  • Kawu Sumaila ya koma APC
  • Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro
  • Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 112
  • Hajjin 2025: Sahun Farko Zai Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki 9 Ga Watan Mayu
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna