An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe
Published: 24th, April 2025 GMT
Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe (AISEB) ta fara rabon tabarmi da gidajen sauro ga almajirai a fadin jihar.
Sakataren Zartarwa na hukumar, Malam Umar Abubakar ya cen tabarmi da gidajen sauron tallafi na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na inganta walwala da rayuwar almajiran makarantun tsangaya a fadin jihar.
A cewarsa, shirin ya yi daidai da umarnin da gwamnatin jihar ta ba hukumar na tabbatar da kulawa da kuma tallafa wa yara almajirai.
Ya bayyana cewa an tsara rabon ga ɗalibai 100 a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar 17, wanda za a fara daga makarantun Goni Yahaya da Goni Muhammad Tsangaya da ke Damaturu.
Ya ƙara da cewa, kayayyakin za su taimaka wa almajirai su kasance da cikin tsafta da walwala, kuma hukumar za ta ƙara kaimi wajan samar da abubuwa kamar su ciyarwa, sutura, da samar da kayayyakin koyo da koyarwa.
A nasa jawabin godiya, shugaban makarantar Goni Muhammad Tsangaya Malam Goni Muhammad ya bayyana tallafi a matsayin wanda ya dace, kuma zai iya canza rayuwar almajiran, yana mai kira ga ƙungiyoyi da ɗaifaikun mutane da su yi koyi da irin wannan matakin.
“Hakan zai taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar ɗalibanmu, musamman wajen hana kamuwa da cututtuka da sauro ke haifarwa da kuma samar da kwanciyar hankali yayin barci,” in ji shi.
Ana sa ran ci gaba da rabon kayayyakin nan da makonni masu zuwa a dukkan kananan hukumomin jihar 17.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙasashen AES sun kafa gidan rediyo don yaƙar farfagandar turawa
Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES), sun sanar da shirinsu na ƙaddamar da gidan rediyo na haɗin gwiwa.
Ƙasashen guda uku, waɗanda duk a halin yanzu suke ƙarƙashin mulkin soja, sun jaddada cewa sun kafa gidan rediyon ne da nufin daƙile farfagandar ƙasashen waje da kuma isar da “ingantattun bayanai na gaskiya” ga ’yan ƙasarsu.
Sanarwar tasu ta kasance bayan ƙaddamar da gidan talabijin ɗinsu na intanet na haɗin gwiwa da suka yi a watan Disamba na 2024, wanda suka bayyana a matsayin dandamali da aka samar domin “yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.”
Baya ga waɗannan ayyukan watsa labarai, a baya ƙungiyar ta nuna sha’awarta ta kafa kamfanin jiragen sama na yankin da kuma bankin saka hannun jari, wanda ya ƙara nuna jajircewarsu ga haɓaka haɗin kai da ci-gaba a tsakanin ƙasashe mambobin AES.
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a NijeriyaA watan Janairu na 2025 ne ƙasashen uku da suka kafa ƙungiyar ta AES, suka sanar da ficewarsu a hukumance daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS).
Makonni uku da suka gabata, ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin sojoji, sun ɗora harajin shigo da kaya na kashi 0.5 bisa ɗari a kan kayayyaki daga ƙasashen ECOWAS.
Harajin ya shafi duk kayayyakin da suka shigo daga ƙasashen ECOWAS zuwa kowace daga cikin ƙasashen uku, banda kayan agajin jin kai.
Wannan tsarin ya yi karo da shirin ECOWAS na tabbatar da zirga-zirgar kayayyaki a tsakanin mambobinta da ƙasashen AES duk da ficewarsu a hukumance daga ƙungiyar a watan Janairu.