Leadership News Hausa:
2025-04-24@19:28:37 GMT

Tabbas Amurka Za Ta Cije A Yakin Haraji Da Ta Kaddamar A Duniya

Published: 24th, April 2025 GMT

Tabbas Amurka Za Ta Cije A Yakin Haraji Da Ta Kaddamar A Duniya

Ban da haka, yadda gwamnatin Trump ba ta da tabbas a kan manufofinta na haraji yana kuma ba kasashen duniya mamaki. Ba a jima ba da gwamnatin Amurka ta sanar da matakinta na harajin ramuwar gayya a kan kasashen da ke ciniki da ita, sai kuma ga shugaba Trump ya sanar da dage harajin a kan wasu kasashe na kwanaki 90.

Kuma kashegari sai aka ji ya yi barazanar cewa, in dai ba a kai ga cimma daidaito a shawarwari ba, to, Amurka za ta maido da harajin. Ban da haka, gwamnatin Amurka ta kuma yi gyara ta ba-zata a kan dokokinta na haraji, inda ta cire harajin ramuwar gayya a kan kayayyakin lataroni da suka hada da wayar salula da kamfuta da sauransu.

 

Haraji abu ne da ya shafi manufar kasa, amma ga shi gwamnatin Amurka ta mai da shi kamar wasa, wanda hakan ya bayyana rashin tunani na manufofin haraji na kasar, da ma yadda take mai da su a matsayin makamai na nuna fin karfi a duniya. Amurka ta ce wai tana neman tabbatar da yi mata adalci ne, amma a hakika kuwa, tana neman kakaba fifikonta ne a kan sauran kasashe.

 

Tabbatar da ci gaba hakki ne ga kowace kasa a maimakon wasu kasashe kalilan. Kasashen duniya na rungumar adalci a maimakon nuna fin karfi. Tabbas Amurka za ta cije a yunkurinta na neman tabbatar da fifikonta a kan sauran kasashen duniya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Sami Lambobin Yabo  8 A Wasan Taekwondo Na Duniya

Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa.

An  fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa.

Daga cikin lambobin yabon din da tawagar ta Iran ta lashe da akwai gwala-gwalai 4, azurfa 3 da kuma tagulla.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kare-Karen Haraji Ba Zai Bunkasa Arzikin Amurka Ba
  • Xi: Yake-yaken Haraji Da Kasuwanci Na Tauye Hakkoki Da Muradun Dukkan Kasashe
  • IMF: Rashin Tabbas Zai Dagula Tattalin Arzikin Duniya
  • Iran Ta Sami Lambobin Yabo  8 A Wasan Taekwondo Na Duniya
  • Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
  • Kungiyar BRICK Ta Rattaba Hannu A Kan Yarjeniyar Raya Ayyukan Noma A Duniya
  • Illolin Da Manufar Haraji Kan Kayayyaki Ta Haifar A Kan Amerikawa
  • Yakin Ciniki Kalubale Ne Kuma Dama Ce Ga Nahiyar Afirka
  • Sin: Matakin Harajin Kwastam Da Amurka Ta Dauka Babakere Ne