HausaTv:
2025-04-24@22:22:47 GMT

Amurka Ta Kai Hare-hare Akan Birane Mabanbanta Na Kasar Yemen

Published: 24th, April 2025 GMT

Jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-haren a kan biranen San,a,Sa’adah da kuma Hudaidah na kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labarun “Saba’a” na kasar Yemen ya nakalto cewa sojojin na Amurka sun kai hare-hare har sau uku a dutsen Naqam, wanda  yake gabashin birnin San’aa.

Kamfanin dillancin labarun na “Saba’a” ya kuma ce, jiragen yakin Amurka din sun kai hare-haren ne a tsakanin marecen jiya Laraba da kuma safiyar yau Alhamis.

Daga cikin wuraren da aka kai wa harin jiya da marecen da akwai Sahlin dake karamar hukumar Ali-Salim. Sau 6 Amurkan ta kai wa yankin hare-hare.

Da safiyar yau Alhamis kuwa jiragen yakin na Amurka sun kai hare-hare a gundumar Sa’adah.

Wasu yankunan da su ka fuskanci hare-haren su ne, al-tahita, dake kudancin gundumar Haudaidah, a yammacin kasar ta Yemen.

Amurka tana kai wa Yemen hare-hare ne saboda  bayar da kariya ga HKI, da zummar hana Yemen kai hare-hare akan manufofin ‘yan sahayoniya a ruwan tekun ” Red Sea”.

Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta bayyana cewa ba za ta taba daina kai wa HKI hare-haren ba har sai idan an daina kai wa Gaza hari. Bugu da kari ta sanar da cewa;za ta ci gaba da hana jiragen ruwa wucewa ta tekun “Red Sea” har zuwa lokacin da za a kawo karshen hana shigar da kayan agaji cikin yankin na Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kai hare hare kasar Yemen

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita

Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne.

Ya kara da cewa: Dogaro da tsarin gwamnatocin Amurka da suka shude kan takunkumin tattalin arziki a kan kasashe masu tasowa, a matsayin makamin tsoratarwa da matsin lamba na siyasa, wani lamari ne da ya saba wa muhimman ka’idojin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma dokokin kasa da kasa, kuma yana yin zagon kasa ga ginshikin doka da ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, kuma yana haifar da keta hakkin bil’adama na asali na al’ummomin da takunkumin ya shafa, musamman ‘yancin ci gaba. Wannan hali sau da yawa yana zama laifi ga ɗan adam.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
  • Kasar Yemen Zata Aiwatar Da Abubuwan Mamaki Da Zasu Firgita Makiyanta Kuma Abokan Gaba
  • Jiragen yakin Amurka sun kara kai hari kan kasar Yemen
  • Sin Ta Ce Ya Kamata Amurka Ta Tattauna Da Ita Bisa Mutuntawa Matukar Da Gaske Take
  • Ba ‘Yan Nijeriya Ne Ke Kai Mana Hare-hare A Benuwai Ba – Gwamna Alia
  • Yawan Falasdinawan Da Suka Yi Shahada Sakamakon Hare-Haren ‘Yan Sahayoniyya Sun Kai 51,266
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna
  • An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 12 a Neja
  • Yakin Ciniki Kalubale Ne Kuma Dama Ce Ga Nahiyar Afirka