Shenzhou-20: Kasar Sin Ta Aike Da ‘Yan Sama Jannati 3 Zuwa Sararin Samaniya
Published: 24th, April 2025 GMT
Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya.
Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya, da kuma girkewa da dawo da na’urorin da aka makala a wajen tashar.
Ya zuwa yanzu dai, ‘yan sama jannatin kasar Sin 26 ne suka yi nasarar zuwa sararin samaniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a sararin samaniya
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Damƙe Mutane 148, Sun Ƙwato Makamai A Adamawa
Ya ƙara da cewa IEDs guda biyu da aka gano an birne su ne yankunan ƙaramar hukumar Hong, kuma an fashe su.
Morris ya kuma ce ‘yansandan sun ceto wasu da aka sace guda shida tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Ya jinjina wa jami’an tsaron da suka taka rawar gani wajen wannan aiki, kuma ya tabbatarwa da jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da tsaro a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp