Gwamnati ta amince ta bai wa mahajjata kuɗin guzirinsu a hannu
Published: 25th, April 2025 GMT
Gwamnatin Najeriya ta amince kuma ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.
Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi wanda ya roƙi shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON.
Hukumar NAHCON a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh, ta dage cewa ɓullo da hada-hadar kuɗi ta amfani da kati zai shafi shirin hukumar na gudanar da ayyukan hajjin 2025.
Shugaban ya damu matuƙa da cewa amfani da katin banki na dole da babban Bankin Najeriya CBN ya gabatar don gudanar da aikin hajji zai kawo tarnaƙi ga tsare-tsare da kuma gudanar da aikin Hajjin bana na 2025.
Bayan ganawar Hukumar NAHCON da Mataimakin shugaban ƙasa, Kwamishinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na NAHCON, Aliu Abdulrazaƙ, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe kuɗaɗensu da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin Bana: Kamfanoni 4 da za su yi jigilar maniyyata — NAHCON
Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta sanar da soma jigilar maniyyatan bana zuwa Saudiyya daga ranar 9 ga watan Mayu yayin da take tabbatar da kammala shirye-shirye aikin Hajjin bana.
Hukumar ta bayyana hakan ne bayan wata ganawa da shugabanta da wakilan majalisar gudanarwa suka yi da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
An daƙile yunƙurin juyin mulki a Burkina Faso Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan mutuwar Fafaroma FrancisMataimakin shugaban kasar ne ya gayyaci shugaban hukumar, Farfesa Abdullah Saleh Usman da wakilan sashen gudanarwa zuwa ganawar a ofishinsa domin sanar da shi inda aka kwana game da shirye-shiryen aikin hajjin.
“Mun yi masa bayani game da shirye-shiryenmu a Makkah da Madina da Arafa kuma ya gamsu, har ma ya ba mu umarnin yadda za mu haɗa kanmu mu yi aikin har zuwa ƙarshensa.”
Kazalika, shugaban ya ce suna sa ran kammala aikin kwashe maniyyatan a ranar 24 ga watan Mayu.
Hukumomi sun ce mutum 43,000 ne za su je aikin Hajjin daga Nijeriya a wannan shekara yayin da a bara mutum kusan 95,000 ne suka yi ibadar.
“A shekarar da ta wuce muna da alhazai 95,000, kamfonin jigila uku muka bai wa aiki. Yanzu da muke da alhazai 43,000, mun ɗauki kamfonin huɗu. To ina maganar ƙarancin jirage a nan?,” in ji farfesan.
Bayanai sun ce kamfonin sufurin jiragen da za su yi jigilar maniyyatan sun hada da Airpeace — 5,128 da Flynas — 12,506, sai Max Air — 15,203 da kuma Umza Air — 10,163.
A ’yan makonnin nan ne ’yan majalisar gudanarwar hukumar suka rubuta wa Kashim Shettima koke, suna zargin shugaban NAHCON, Farfesa Abdullah Saleh da mayar da su saniyar ware wajen gudanar da lamurran hukumar, zargin da shugaban ya musanta.
Hotunan ganawar wakilan NAHCON da mataimakin shugaban kasa: