Faransa ta jaddada aniyarta na ci gaba da tattaunawar nukiliyar iran
Published: 25th, April 2025 GMT
Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran.
A yayin taron manema labarai na mako-mako a birnin Paris, Christophe Lemoine ya jaddada cewa: “Muna ci gaba da jajircewa wajen warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa da Tehran.”
Wannan bayanin na zuwa ne bayan da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewa, Tehran a shirye ta ke ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai, inda ya bayyana cewa tattaunawar za ta iya bude wata sabuwar hanya.
Araghchi ya bayyana cewa, bayan shawarwarin baya-bayan nan da aka yi a Moscow da Beijing, a shirye yake ya ziyarci Paris, Berlin da London.
Ya kuma ce tun kafin fara tattaunawar da Amurka, Iran na shirye, amma kasashen Turan uku da batun ya shafa ba su nuna sha’awarsu ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ci gaba da tattaunawa nukiliyar Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Yemen Zata Aiwatar Da Abubuwan Mamaki Da Zasu Firgita Makiyanta Kuma Abokan Gaba
Jami’in kasar Yemen ya jaddada cewa: Kwanaki masu zuwa za su aiwatar da abubuwan mamaki da za su ba abokan gabanmu mamaki!
Daraktan sashin yada labarai na fadar shugaban kasar Yemen Zaid Al-Gharsi ya jaddada samun gagarumin ci gaba a karfin sojojin kasar Yemen musamman a fannin fasaha da makamai. Ya yi nuni da cewa, kasar Yemen na gab da samar da sabbin makamai da za su bai wa kowa mamaki.
A cikin wata hira da tashar talabijin ta Al-Alam, Zaid Al-Gharsi ya yi magana game da irin goyon bayan da kasar Yamen ke ba wa yankin Zirin Gaza, inda ya yi nuni da mahimmancin hare-haren soji kai tsaye kan makiya ‘yan sahayoniyya tare da jaddada fifikon karfin kasar Yemen idan aka kwatanta da na ‘yan sahayoniyya da Amurkawa.
Al-Gharsi ya bayyana cewa, yakin da ake yi a halin yanzu yana da manyan fasahohi, saboda makiya ‘yan sahayoniyya sun mallaki fasahar soji na zamani da kuma dogaro da goyon bayan Amurka.