Wani kwararre a fannin lafiya da ke aiki da asibitin koyarwa na Aminu Kano ya ce bisa kididdigar baya-bayan nan sama da mutane miliyan 11 ne ke dauke da ciwon suga a Najeriya, wasu da dama kuma ba a gano su ba.

 

 

 

Farfesa Zuba Ilyasu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron shekara-shekara na kungiyar likitocin endocrinologists of Nigeria (ACEN) karo na 14, wanda ya gudana a Tahir Guest Palace Kano.

 

 

 

Farfesa Ilyasu ya yi nuni da cewar akwai bukatar wayar da kan jama’a game da salon rayuwa da ake bukatar a yi amfani da su wajen magance matsalar ciwon suga da kuma kiba.

 

 

Shugaban taron, Emeritus Farfesa Musa Borodo, ya yi tir da tsadar hanyoyin samar da kiwon lafiya a kasar nan, inda ya jaddada bukatar da ake da shi na samar da dabarun rage radadin cututtuka kamar kiba da ciwon suga.

 

 

 

Borodo ya lura cewa taron zai gyara hanyoyin da za a fadakar da jama’a kan salon rayuwa da kuma rigakafin cututtuka.

 

 

Shugaban ACEN, Dr. Williams Balogun, ya bayyana bukatar gwamnati da masu ruwa da tsaki su kara saka hannun jari wajen magance matsalolin cututtuka masu yaduwa.

 

 

Ya kuma jaddada kudirin kungiyar na samar da dabarun magance matsalar ciwon suga da kiba.

 

 

 

“Wannan taron zai bayyana ra’ayoyi da bincike iri-iri da nufin tabbatar da cewa an magance wadannan illoli na ciwon suga da kiba sosai.” –

 

Da yake jawabi a lokacin taron Gwamna Abba Kabir wanda kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf ya wakilta ya ce taron ya zo kan lokaci.

 

Ya ce gwamnatin jihar Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hada kai da kungiyoyin likitoci kamar ACEN da nufin hada kai don magance ciwon suga da kiba kasancewar su cututuka masu kalubale.

 

Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga mahalarta taron da su fitar da kudurori da za su magance yawaitar cutar siga da kiba.

 

Taron na da nufin bayyana ra’ayoyi daban-daban da binciken bincike don magance barazanar ciwon sukari da kuma kiba.

 

 

Taron ya ja hankalin mahalarta daga dukkan sassan tarayyar.

 

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Taro

এছাড়াও পড়ুন:

Kada ku karaya da shigo da abinci daga ƙasar waje — IAR

Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya ta hori manoma da kada su yi fargaba bisa yadda Gwamnatin Tarayya ke shigo da abinci daga ƙasashen waje.

Shugaban Cibiyar, Farfesa Ado Yusuf ya ba da shawarar ce a yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron bita da tsare-tsaren aikin noma na shekarar 2025 da ya gudana a dakin taro na Tanimu Balarabe da ke Cibiyar IAR Samaru, Zaria.

Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato

Ya tunasar da manoma cewa, nau’o’in abincin da suke nomawa ba a kasar nan kadai ake amfani da su ba, don haka kayan amfanin gonarsu zai ci gaba da daraja a wasu sassa na kasashe duniya da suke neman su.

Farfesa Yusuf ya kara da cewa, har yanzu abubuwan da ake nomawa a kasar nan ba ya wadatar da bukatun ‘yan kasa ballantana a rasa yadda za a siyar da su.

Sai dai kuma shugaban cibiyar ya yi kira da a dauki matakan da suka dace wajen kayyade irin kayan abincin da ake shigowa da su don cim ma burin da ya sa gwamnati ta dauki matakin.

Masanin aikin gonar daga nan sai ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta wadata manoma da muhimman kayan aikin noma, domin ci gaba da ba su ƙwarin gwiwar aikin gona, domin kada shigowa da kayan abincin ya karya masu gwiwa.

Ya tabbatar da cewa, duk da kokarin gwamnati na shigowa da abinci daga waje, wanda ya karya farashin kayan abinci, manoma sun sami ribar noma daidai gwargwado a daminar bara.

Farfesa Yusuf ya ƙara da cewa, “ina cikin masu son ganin manoma sun sami ribar noma, amma kuma ba na son ganin an tsawwalawa wa jama’a ta inda farashin kayan abinci zai hana talaka sayen abin da zai ci.”

Shugaban Cibiyar IAR ya kara da cewa, duk da Nijeriya na shigowa da kayan abinci, har yanzu ana kuma safarar kayan gona zuwa wasu ƙasashen waje, don haka ya jaddada buƙatar da ke akwai ta samar da ingantattun kayan aikin noma kuma cikin farashi mai rahusa da manoma za su iya mallaka.

Ya bayyana cewa, hauhawar farashi da tsadar kayan noma na iya hana manoma noma isasshen abinci ga kasa, wanda haka zai iya sanadin durkushewar mafi yawa daga cikinsu kuma ya sa su watsar da aikin gona.

Don haka ya roƙi gwamnatin da ta gaggauta ɗaukar matakan sauƙaƙa wa manoma da ribanya ƙwazonsu da wadata ƙasa da abinci.

Da yake tsokaci dangane da ayyukan cibiyar, Farfesa Yusuf ya ce, a wannan shekara ta 2025, cibiyar za ta gudanar da ayyukan bincike a kan aikin noma har sama da guda 180, yayin da za ta bai wa wasu aikace-aikacen gona 32 muhimmanci don bai wa manoma ingantattun dabaru tare da sauke nauyin da ke kan cibiyar na habaka aikin noma a kasa.

Tun farko da yake nasa jawabin, shugaban taron kuma Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Kabir Bala ya ce, duk da dai yana halartar taron ne a karo na karshe a matsayinsa na shugaban jami’ar duk da haka cibiyar za ta ci gaba da samun dukkan taimako da kwarin gwiwar da take bukata daga gare shi.

Farfesa Bala wanda ya nuna jin dadinsa bisa yadda aka tattara masana aikin gona daga jihohi daban-daban na kasar nan, inda ya yi fatan za a fito da wata matsaya da za a habaka samar da abinci da kuma saukaka wa ‘yan kasa yadda za su same shi cikin sauki kuma a wadace.

Sai dai kuma ya roki gwamnati da ta samar da karin kudade ga cibiyar don ci gaba da gudanar da ayyukan binciken sababbin dabarun aikin gona.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jiragen Kasa Na Sin Sun Yi Jigilar Fasinjoji Sama Da Miliyan 100 A Lokacin Hutun Ranar Ma’Aikata
  • Za A Gudanar Da Taron Tallata Fim Din “Red Silk” A Moscow
  • Iran da Saudiyya sun jaddada bukatar kare hurimin kasar Siriya
  • NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka
  • Kada ku karaya da shigo da abinci daga ƙasar waje — IAR
  • An Yi Kira Da A Dauki Kwakkwaran Matakin Magance Rashin Tsaro
  • Kiwon Lafiya: Jihar Kwara Ta Bayyana Yadda Karancin Likitoci Ke Kawo Mata Cikas
  • Ma’aikatar Lafiya Ta Falasdinu Ta Tabbatar Da Karuwan Falasdinawan Da Suka Yi Shahada
  •  Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-haren HKI Akan Syria Da Nufin Rusa Kasar
  • An kama masu garkuwa da mutane 3 da kuɓutar da wasu