Kudaden Da Ke Hannun Mutane Sun Ragu Zuwa Naira Tiriliyan 5 – Rahoto
Published: 25th, April 2025 GMT
Raguwar kudin a hannun mutane na iya zama wani bangare na kokarin rage matsin lamba kan hauhawar farashin kayayyaki da samun daidaiton tattalin arziki.
Baya ga raguwar kudade a hannun mutane, ajiyar a bankin CBN ya karu zuwa naira biliyan 28.52 a watan Maris na 2025, daga naira biliyan 27.57 a watan Fabrairun 2025.
A halin yanzu, ajiyar ko-ta kwana ba ta canza ba a naira miliyan 284.36 a cikin watanni uku.
Ajiyar banki yana nufin kudaden da Babban Bankin da bankunan kasuwanci ke rike da shi don tabbatar da hada-hadar kudade a cikin bangaren banki. Ci gaba da karuwar ajiyar bankuna wata alama ce ta kokarin CBN na tsare harkokin kudade da daidaita tattalin arziki.
Ya daidai wannan lokacin a bara, an bayyana cewa darajar kudin Nijeriya da ke yawo a hannun mutane ya karu zuwa naira tiriliyan 3.87 a karshen watan Maris na 2024.
Wannan ya nuna karuwa daga naira tiriliyan 3.69 a watan Fabrairu da naira tiriliyan 3.65 a watan Janairu. Bugu da kari, kudin da ke wajen bankuna kuma ya karuwa a cikin kwata na farko, ya karu daga naira tiriliyan 3.28 a watan Janairu zuwa naira tiriliyan 3.41 a watan Fabrairu, kuma ya kai naira tiriliyan 3.63 a watan Maris.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: naira tiriliyan 3
এছাড়াও পড়ুন:
Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 112
112-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko.
A cikin shirimmu da ya gabata mun kawo maku yadda Abuzar a Alghifari babban sahabin manzon All..(s) wanda ya kasance daga cikin mutane na farko da suka musulunta a Makka, sannan ya kuma garinsu giffar yana kiran mutane zuwa ga addinin musulunci har zuwa lokacinda manzon All..(s) yayi hijira, zuwa Madina sai shi ma yayi hijira. Banda haka, manzon All..(s) ya yabeshi a cikin hadisai da dama saboda tsoron All..ta zuhudu da kuma sanin addini.
Amma a lokacinda Uthman bin Affan ya zama khalifa ya kuma dora danginsa Banu Umayya a kan al-ummar musulmi suna azabtar da shi suna kuma kwasar kudaden jama’a suna kashewa kansu, ya fuskanci matsaloli da sahabban manzon All..(s) da dama daga ciki har da Abuzar Alghiffari, wanda ya ci gaba da sukar khalifa da kuma danginsa, har sai da ya kore shi daga madina zuwa Sham da farko, sannan ya sake dawo da shi Madina a cikin mummunan hali, amma Abuzar bai dandara ba, ya ci gaba da sukansu har sai da wata rana, Khalifa yayi tambaya a kan al-amuran addini sai wani bayahude wanda bai dade da musulunct ba, ya bada amsa kuma ba dai dai ba, sai Abuzar ya tashi a kasansa, sai Khalifa kuma ya tashi a kan Abuzar yana masa tsawa, daga karshe ya sake korarsa daga Madina karo na biyu, amma a wannan karon ya kore shi zuwa wani daji inda babu mutane, kuma yace zai zauna a wurin har sai ya mutunu.
Munji yadda ya umurci Marwan dan hakam, ya bashi guzuri ya koma can inda ba zai ga wani ba, kuma ba wanda zai ganshi. Sai Marwan ya ajiye shi a wani wuri kafin ya kammala hada masa guzuri, sannan khalifa ya fadawa Marwan ya fitar da shi cikin kaskanci daga Madina sannan kada ya bar kuma ya yi magana da shi.