Aminiya:
2025-04-25@14:12:13 GMT

Gwamnan Kano ya kafa sabbin hukumomi 4

Published: 25th, April 2025 GMT

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki guda huɗu da suka kafa muhimman hukumomi domin ƙarfafa tsarin gudanarwa na jihar da kuma haɓaka ci gaba mai ɗorewa.

Waɗannan dokokin za su samar da Hukumar Kare Hakkokin Jama’a ta Jihar Kano (KASPA), Hukumar Kula da Tallace-tallace da Rubuce-rubuce ta Jihar Kano (KASIAA), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Zamani ta Jihar Kano (KASITDA), da kuma Hukumar Bunƙasa Ƙananan Kasuwanci da Matsakaita ta Jihar Kano (KASMEDA).

Gwamna Abba, ta bakin mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana muhimmancin waɗannan dokokin wajen ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, tallafa wa ƙananan kasuwanci, tsara tallace-tallace, da inganta kare hakkin jama’a da samar da ayyuka.

Ya jaddada cewa waɗannan hukumomi za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, jawo jari, da kuma aiwatar da tsare-tsaren gwamnati yadda ya kamata, wanda ya nuna  hangen nesansa na sanar da Kano ta zamani da bunƙasa tattalin arziki.

Ƙarin ’yan Najeriya za su shiga talauci nan da 2027 — Bankin Duniya ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa 

Gwamnan ya yi gargaɗi game da keta waɗannan sabbin dokokin, yana mai cewa za a hukunta duk wanda ya karya su da tsauraran matakai domin tabbatar da bin doka da oda.

Kafa waɗannan hukumomi ya nuna ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da gyara cibiyoyin gwamnati, inganta gudanarwa, da kuma sanya Kano a matsayin cibiyar da ta fi fice a fannin ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci, da ci-gaba mai ɗorewa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Tattalin Arziki ta Jihar Kano

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙasurgumin Ɗan Fashin Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Mutu Bayan Arangama Da ‘Yansanda A Kano

Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti.

 

“An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar.

 

Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin.

 

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.

 

Ya kuma yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi ko su bayar da bayanan da za su kai ga kama wadanda ake zargin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jigawa Ta Bude Sabon Babi: Maniyyata Za Su San Masaukansu Tun Daga Gida Najeriya
  • Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shirin Tsaftar Muhalli Na Wata Wata Saboda Jarrabawar JAMB
  • Baffa Bichi, Kabiru Rurum, Sha’aban Sharada Da Wasu Sun Koma Jam’iyyar APC
  • Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni
  • An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe
  • 2025: NAHCON Ta Ware Kujerun Aikin Hajji 1,407 Ga Jihar Taraba
  • Ƙasurgumin Ɗan Fashin Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Mutu Bayan Arangama Da ‘Yansanda A Kano
  • Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna