HausaTv:
2025-04-25@15:15:46 GMT

Iran Ta Musanta Zargin Nethalands Na Cewa Tana Da Hannun A Kokarin Kisa A Kasar

Published: 25th, April 2025 GMT

Ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Netherlands ta yi watsi da zargin da gwamnatin kasar takewa JMI na kokarin aiwatar da kashe-kashe har guda biyu a shekarar da ta gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tace Ofishin jakadancin Iran da ke Netherlands  ta fidda wannan sanarwan ne a jiya Alhamis.

Ta kuma kara da cewa, kasar Iran wacce ta fi ko wace kasa a duniya fama da yan ta’adda, ba za ta yi kokarin kasashe wani a wani wuri ba.

Sanarwan ta bayyana cewa wannan al-amarin siyasace ta tsakanin jami’an siyasa na kasar ta Netherlands  don neman amincewar masu kuri’a.

Kafin haka dai wata cibiyar ayyukan tsaro ta kasar Netherlands  mai suna AIVD ta bada rahotomta na shekara shekara kan abinda ya shafi ayyukan ta’addancin inda ta ammabi kasar Iran a ciki.

Har’ila yau wannan rahoton yasa ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Netherlands  ta kira jakadan JMI a kasar zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar don gabatar da korafinta.

Gwamnatocin kasashen Turai musamman kasar Faransa tana gudanar da taron yan adawa da JMI a kasashensu, wadanda kuma sune suka kashe Iraniyawa da dama a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a kasa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Haramtacciyar Isra’ila Tana Azabtar Da Falasdinawa A Gidajen Kurkukunta

Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba

Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila.

Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza.

Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda ake tsare da su da hakan ke kara masifar azabtarwar da ake gana musu. Haka kuma wanda ake tsare ana yi masa fyade a gaban ’yan uwansa da ake tsare da su, da nufin wulakanta shi da kuma rusa tunaninsa, da hakan ke kara tsoro da firgici a tsakanin sauran wadanda ake tsare da su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe
  • Duniyarmu A Yau: Shiri Kasashen Yamma Na Kashe Dukkan Falasdinwa A Gaza
  • Kudaden Da Ke Hannun Mutane Sun Ragu Zuwa Naira Tiriliyan 5 – Rahoto
  • Gwamnatin Haramtacciyar Isra’ila Tana Azabtar Da Falasdinawa A Gidajen Kurkukunta
  • Arakci: Mun Yi Tattaunawa Mai Kyau Da Mahukuntan Kasar China
  • Iran ta jaddada cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Gudanar Da Tattaunawa Kan Tsaronta Ba
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana China Da Rasha A Matsayin Abokai Na Tushe Ga Iran
  • Iran ta ce an dage tattaunawar matakin kwararru da Amurka zuwa ranar Asabar
  • Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Matashin Da Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kano