Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta bullo da tsarin da kowanne maniyyaci zai san masaukinsa a kasa mai tsarki tun daga nan gida najeriya.

Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shalkwatar hukumar dake Dutse.

Yana mai cewar, wannan shi ne karon farko da hukumar ta bullo da tsarin domin maniyyaci ya san masaukinsa a nan gida kafin zuwa kasa mai tsarki.

Game da batun kudade kuwa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma kaddamar da kwamitin canjin kudaden guzuri na maniyyata domin samun saukin canji yayin aikin Hajjin.

Ya ce an kafa kwamitin ne domin  bibiyar maniyyata kan canjin kudin guzuri, kasancewar wasu batagari na damfarar mahajjata a kasa mai tsarki wajen canjin kudade daga Dala zuwa Riyal.

Ya kara da cewar, hukumar ta turawa hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON fiye da naira miliyan dubu shida da miliyan dari uku da talatin da daya (6,331,000,000) a matsayin kudaden maniyyatan aikin hajjin bana.

Ya ce jihar Jigawa ce ta farko wajen biyan kudaden aikin hajjin bana ga hukumar aikin hajji ta kasa.

Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar Gwamnatin jihar ta baiwa hukumar rancen naira miliyan dubu uku da miliyan dari uku da sittin (3,360,000,000) da ta yi amfani da shi wajen sayen kujerun aikin hajjin bana daga hukumar aikin hajji ta kasa.

Umar Labbo, ya ce sun cimma kaso 95 bisa 100 na aikin bada biza ga maniyyata.

Babban Daraktan ya shedawa mahalarta taron cewar hukumar ta kammala duk wani shiri na fara jigilar maniyatan  wanda za a fara jigilar alhazan Najeriya a ranar tara ga watan Mayu.

Kazalika, wakilan hukumomin tsaro sun yi bayani akan shirye shiryen da suke yi domin tunkarar aikin hajjin bana

Ya kuma yi kira ga maniyyatan jihar, da su ci gaba da halartar cibiyoyin bita domin samun ilimin da za su gudanar da aikin hajji cikin sauki.

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

An Umurci Sojoji Su Kawarda ‘Yan Bindiga Daga Kwara Da Niger A Cikin Wata Daya

Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.

 

A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22  a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba.

 

A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar.

 

Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda.

 

Oluyede ya kara da cewa, rundunar soji ta samar da Uniform guda 100,000 yayin da aka ware naira miliyan dubu domin ciyar da sojojin a kowane wata.

 

A kwanakin baya ne wata kungiyar da aka fi sani da Mahmuda ta bulla a kananan hukumomin Kaiama da Baruten na jihar Kwara yayin da wasu da ba a tantance ba suka kashe mutane bakwai a Ilesha Baruba da ke karamar hukumar Baruten a jihar Kwara ranar Litinin.

COV/ALI RABIU

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni
  • An Umurci Sojoji Su Kawarda ‘Yan Bindiga Daga Kwara Da Niger A Cikin Wata Daya
  • 2025: NAHCON Ta Ware Kujerun Aikin Hajji 1,407 Ga Jihar Taraba
  •  Ghana Ta Fada Cikin Takaddama Bayan Tisge Babbar Mai Shari’a Ta Kasar Da Shugaban Kasa Ya Yi
  • Al’ummar Gaza Suna Tsananin bukatar Agaji Da Kiran A Tilastawa Gwamnatin Mamayar Isra’ila Bude Mashigar Yankin
  • Hajjin Bana: Kamfanoni 4 da za su yi jigilar maniyyata — NAHCON
  • Hajjin 2025: Kashim Shettima Ya Jinjinawa Hukumar Alhazai Bisa Matakan Da Ta Dauka
  • Hajjin 2025: Sahun Farko Zai Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki 9 Ga Watan Mayu
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna