An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi
Published: 25th, April 2025 GMT
Wasu mutane 13 sun faɗa a komar ’yan sanda ka zargi da zubar da ciki da kuma mutuwar wata budurwa ’yar shekara 18 a Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ana tuhumar huɗu daga cikin mutanen da aikata laifin fyade, zubar da ciki da kuma mutuwar budurwa a garin Misau da ke Ƙaramar Hukumar Misau.
Wakil ya ce, a ranar 4 ga Afrilu, 2025 sun samu bayanai ewa, kimanin watanni hudu da suka gabata, wasu matasa biyu a yankin Lariski da ke Misau, sun kama wata yarinya mai shekaru 18 da suka yi ta yi lalata da ita sau da yawa.
Ya ce a lokacin da suka lura tana ɗauke da juna biyu, sai suka nemi wani mutum suka ba shi naira 40,000 don ya taimaka musu wajen zubar da cikin, amma abin takaici sai aka samu matsala wanda a qarshe ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Wakil ya ce, “Bayan an yi mata allurar zubar da ciki saita fita daga hayyacinta, daga baya kuma ta kamu da rashin lafiya. Hakan ya sa danginta suka kai ta Babban Asibitin Misau, daga baya an mika ta zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Azare, inda hukumomin asibitin suka sanar da cewa ta mutu a lokacin da take jinya.”
Bayan samun rahoton, an kama wadanda ake zargin, inda suka amsa laifin da suka aikata tare da ambaton wasu da ke da hannu a lamarin. Ya ce sauran wadanda ake zargin da wasu mutum huɗu suna hannun ’yan sanda ana bincike.
Bayan haka kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa laifukan da suka aikata.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Zubar da ciki zubar da ciki
এছাড়াও পড়ুন:
An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure
Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta sallami ɗaya daga cikin malamanta, Dokta Usman Mohammed Aliyu daga jami’ar bisa zargin neman yin lalata da wata ɗaliba matar aure da ke karatun digiri na biyu.
Idan dai ba a manta ba, Kamila Rufa’i Aliyu, ɗalibar Sashen koyon aikin injiniya ce, a shekarar bara ta roƙi mahukuntan Jami’ar ta hannun tsangayarsu da su binciki lamarin.
Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka saceƊalibar ta kuma zargi Dakta Aliyu da yi mata barazanar rashin samun nasarar karatunta idan har ta ƙi amincewa da biyan buƙatarsa.
Malamin da ya samu labarin ƙarar da aka shigar da shi, an shigar da ƙarar a gaban kotu a kan zargin ɓata suna a kan wata ɗaliba, tsangayar da Jami’ar.
Amma Jami’ar a cikin Jaridarta (ATBU Herald) ta Afrilu 22, bugu na Vol. 39 lamba ta 5 ta bayyana cewa majalisar gudanarwa ta jami’ar ta kori Dakta Usman Mohammed Aliyu daga aiki a jami’ar.
Jaridar ta ce: “A zamanta na yau da kullun karo na 96 da aka gudanar a ranar Juma’a, 11 ga Afrilu, 2025, Majalisar ta amince da korar Dakta Aliyu bisa laifin neman yin lalata da ɗalibar.”
Rahoton ya ce korar ta biyo bayan wani rahoton da kwamitin ladabtarwa na manyan ma’aikatan ya yi wanda ya same shi da aikata laifin.
“Sanarwar ta ci gaba da cewa korar ta biyo bayan babi na 3, sashi na 1, (o) na sharuɗɗan manyan ma’aikatan jami’ar.