An Sako Malamin Kiristan Cocin Katolika Da Aka Sace A Kaduna
Published: 25th, April 2025 GMT
Farfesa Ibrahim Amos, wani Malamin cocin Katolika, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Kaduna, bayan an sace shi a ranar Alhamis, 24 ga Afrilu, 2025, daga gidansa a St. Gerald Quasi Parish, Kurmin Risga, ƙaramar hukumar Kauru.
Wani shugaba a ɗariƙar dake Kafanchan, Rev. Fr. Jacob Shanet, ya tabbatar da sakin farfesan a cikin wata sanarwa da aka mikawa manema labarai.
Rev. Fr. Shanet ya gode wa jama’ar alheri, da ƙungiyoyin addini, da jami’an tsaro, da sauran masu ƙoƙarin ganin an sake shi. Ya jaddada cewa, goyon bayan da aka samu daga kowanne ɓangare ya tabbatar da cewa ba su kaɗai ke ƙoƙarin tabbatar da darajar rayuwar dan Adam ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Zulum Ya Ƙaddamar Da Aikin Gina Titi Da Gadar Sama Ta Huɗu A Borno
A jawabin Gwamna Zulum wajen kaddamar da aikin titin, ya ce, “A ci gaba da tsarinmu na sabunta birane, a yau mun kaddamar da gina titi mai tsawon kilomita 7.1 daga tashar borno Express zuwa Molai, hadi da karin ginin gadar sama ta hudu.
“Abin da muke da burin aiwatar wa, shi ne ba don kawai kyawawan ayyuka ba, har ma don daukar nauyin ci gaban al’ummar Maiduguri, kuma ya zama dole mu fadada birnin Maiduguri.”
Gwamna Zulum ya yi kira ga yan kwangilar su tabbatar da bin ka’idojin inganci da kuma kammala aikin a cikin lokacin da aka kayyade.
“Za a kammala aikin cikin watanni goma, an bayar da kwangilar kan naira biliyan 16, kuma mun biya kashi 50% na wannan adadin kudin. Don haka, muna kira ga yan kwangilar cewa, ba su da wani uzuri na bata lokacin aikin. Mun kuma ajiye sauran Naira biliyan 8, za a biya a lokacin da aikin ya kammala.” In ji Zulum.
A nashi bangaren, Kwamishinan Ayyuka da Gidaje a jihar borno, Injiniya Mustapha Gubio, ya bayyana cewa, gadar saman za ta hada sabuwar hanyar ta bangarorin biyu na kogin Ngada-bul.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta sa ido kan ayyukan, tare da tabbatar da bin dukkan ka’idojin kwangila.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp