Aminiya:
2025-05-07@00:59:57 GMT

An kama mutum 2 ɗauke da ƙwayar tramadol ta N150m a Kano

Published: 25th, April 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama aƙalla mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, wanda suka hada da: Muntari Shu’aibu da Imrana Rabi’u.

A wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu waɗanda ake zargin ɗauke da ƙunshi guda shida na miyagun ƙwayoyin  Tramadol da aka ƙiyasta kuɗinsu ya haura Dala 92,000 (kimanin Naira miliyan 150m).

Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe Gwamnan Kano ya kafa sabbin hukumomi 4

Bakori ya ce, “Rundunar ’yan sandan ta gudanar da wani samame ta hanyar fasaha da bayanan sirri, ta kama waɗanda ake zargin da wannan miyagun ƙwayoyin, biyo bayan wani rahoto da aka samu.”

Ya ƙara da cewa, kama wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na magance musabbabin munanan laifuka a jihar.

Ya ci gaba da cewa, “aikin ya biyo bayan ƙoƙarin da hukumar ta yi na daƙile ayyukan ta’addanci, waɗanda a cewarsa, galibin safarar muggan ƙwayoyi ne na sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar.”

Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa an miƙa waɗanda ake zargin ga hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa reshen Jihar Kano domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban ƙuliya.

“Wannan ya yi daidai da tsarin Sufeto-Janar na ‘yan sanda na aikin ‘yan sanda da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro a tsakanin ƙungiyoyin tsaro,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Tramadol miyagun ƙwayoyi

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu

Ya gode wa jami’an tsaro da ‘yan banga bisa ƙoƙarinsu, amma ya buƙaci su ƙara ƙaimi don hana faruwar irin haka a gaba.

Shugaban ya kuma buƙaci shugabannin al’umma, jami’an tsaro da mazauna yankin su haɗa hannu don kawo ƙarshen rikicin da tabbatar da zaman lafiya.

Gyang ya roƙi Allah Ya bai wa iyalan waɗanda suka rasu haƙuri rashin su, tare da umartar ma’aikatan lafiya su gaggauta bai wa wadanda suka jikkata kulawar gaggawa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kama Amarya Kan Zargin Kashe Mijinta Bayan Kwana 9 Da Aurensu A Kano
  • Matashi ya kashe mahaifinsa da adda a Jigawa
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 6 A Ƙauyukan Filato, Sun Jikkata Wasu
  • An kashe mutum 6 a sabon hari a Filato
  • EFCC Ta Kama Matashi A Kaduna Bisa Zargin Wulaƙanta Naira A Bidiyon Barkwanci
  • ‘Yansanda Sun Kama Matashi Kan Zargin Kashe Mahaifinsa Har Lahira A Jigawa
  • ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano
  • ’Yan fashi sun kashe magidanci a Kano
  • An Kama Wani Ɗan Ghana Bisa Zargin Kai Mata Hajji Ba Tare Da Lasisi Ba
  • Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga 3, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace