Ministan harkokin wajen Iran ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a yau domin gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa: A yau ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a karkashin jagorancin tawagar diflomasiyya da fasaha don shiga zagaye na uku na shawarwarin da ba na kai tsaye ba da Amurka ta hanyar shiga tsakanin mahukuntan Oman.

Baqa’i ya bayyana cewa: Bangarorin biyu sun amince da gudanar da tarukan fasaha tare da halartar manyan jami’an shawarwari, yana mai bayanin cewa “bisa tsarin da Oman ta shirya da kuma hadin gwiwa tsakanin Iran da Amurka, za a gudanar da tarukan fasaha da shawarwari kai tsaye tsakanin ministan harkokin wajen Iran da wakilin shugaban Amurka na musamman a ranar Asabar.”

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaban da ake samu a shawarwarin yana bukatar daya bangare ya nuna kyakykyawar fahimta, da gaske, da kuma hakikanin gaskiya, yana mai jaddada cewa: Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi aiki ne bisa gogewar da ta gabata da kuma dabi’ar daya bangaren, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cimma halaltacciyar hakki da muradun al’ummar Iran.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: harkokin wajen Iran

এছাড়াও পড়ুন:

Iran ta jinjinawa Sin da Rasha a matsayin kawayenta na kut-da-kut

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing domin yin shawarwari da manyan jami’an kasar Sin, gabanin yin tattaunawa zagaye ta uku da Amurka kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Abbas Araghchi ya shaida wa kafar yada labaran Iran a babban birnin kasar Sin a ranar Laraba cewa, “Sin da Rasha abokan hulda ne na kut da kut da suka tsaya tare da mu a lokutan wahala, don yana da kyau da ma’ana mu ci gaba da tuntubar juna tare da su a bangarori daban-daban, musamman ma yanzu da ake tattaunawa da Amurka.”

“Ya zama dole mu sanar da abokanmu a kasar Sin cikakken bayani game da al’amuran da ke gudana tare da tuntubarsu.” Inji shi.

Yayin da yake jaddada cewa, ya yi irin wannan ganawa da manyan jami’an kasar Rasha a birnin Moscow a makon jiya, Araghchi ya ce yana fatan samun kyakkyawar tattaunawa da mahukuntan Beijing, domin isar da sakon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ga mahukuntan kasar Sin.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce, “A baya kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kuma mai ma’ana a batun nukiliyar kasar Iran, kuma ko shakka ana bukatar hakan.

Za mu ci gaba da tuntubar Sin a matsayinta na mamba a kwamitin sulhun MDD, mamba a kwamitin gudanarwar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, bugu da kari kawa  ta kut-da-kut ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inji ministan harkokin wajen kasar ta Iran.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diflomasiyya
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasarsa A Shirye Take Ta Sulhunta Tsakanin Pakistan Da Indiya
  • Faransa ta jaddada aniyarta na ci gaba da tattaunawar nukiliyar iran
  • Iran ta jinjinawa Sin da Rasha a matsayin kawayenta na kut-da-kut
  • Arakci: Mun Yi Tattaunawa Mai Kyau Da Mahukuntan Kasar China
  • Iran ta jaddada cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Gudanar Da Tattaunawa Kan Tsaronta Ba
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana China Da Rasha A Matsayin Abokai Na Tushe Ga Iran
  • Iran ta ce an dage tattaunawar matakin kwararru da Amurka zuwa ranar Asabar