Shin Manchester United Za Ta Iya Lashe Kofin Europa League?
Published: 26th, April 2025 GMT
Manchester United ta kai zagayen kusa da karshe ne bayan doke Olympic Lyon ta Faransa da 5-4, bayan an yi canjaras da 2-2 a wasan farko da aka buga a Faransa. Kenan United ta yi nasara da 7-6 jimilla. Yanzu United za ta fafata wasan gab da na karshe ne da kungiyar Athletic Bilbao a ranar 21 ga watan Mayu.
Kungiyar ta Bilbao ta kai wasan karshe a gasar Europa sau biyu, na karshen a shekarar 2012, lokacin da Atletico Madrid ta doke ta da ci uku da nema a Bucharest.
Shekara 13 ke nan rabon United ta hadu da Athletic Bilbao, inda kungiyar ta Sifanya ta doke United da 2-1 a gasar ta Europa a shekarar 2012. Ita kuma United wannan ne karo na biyu da za ta buga wasan gab da na karshe a gasar Europa a shekara hudu.
A wancan karon, Manchester United ta doke Roma da ci 8:5 jimilla sai dai kungiyar Billareal ta doke ta a wasan karshe a bugun fanareti bayan an tashi wasan kunnen-doki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Congo Da M23 Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun amince su dakatar da faɗa a gabashin ƙasar har sai an kammala tattaunawar sulhu da ke gudana a halin yanzu wanda Qatar ke shiga tsakani.
Wannan dai ita ce yarjejeniyar sulhu ta baya-bayan nan tun bayan da ƴan tawayen suka ƙara kai farmaki a gabashin ƙasar inda hukumomi suka ce an kashe mutane 7,000 tun daga watan Janairu.
A ranar Larabar da ta gabata ce, ɓangarorin biyu suka ba da sanarwar yin aiki tare don samar da zaman lafiya, bayan shafe sama da mako guda suna tattaunawa, wanda suka ce an gudanar cikin aminci tare da mutunta juna.
A watan da ya gabata, shugaban ƙasar Congo Félix Tshisekedi da takwaransa na Rwanda Paul Kagame suma sun jaddada aniyarsu ta tsagaita wuta ba tare da sharaɗi ba a wata ganawar ba-zata da suka yi a birnin Doha.
Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana gwabzawa ya ƙara kamari ne a watan Janairu, lokacin da ƙungiyar M23 ta ƙaddamar da wani farmaki da ba a taɓa ganin irinsa ba, inda ta ƙwace garuruwan Goma da Bukavu – manyan biranen ƙasar Congo guda biyu, lamarin da ya haifar da fargabar ɓarkewar yaƙi yankin baki ɗaya.
DR Congo na zargin Rwanda da bai wa ƙungiyar M23 makamai tare da tura dakaru domin tallafawa ƴan tawayen.
Duk da ikirarin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka yi, Rwanda ta musanta zargin da ake yi ma ta na goyon bayan ƙungiyar M23.