2027: Babu Dan Takarar Da Zai Iya Cin Zabe Ba Tare Da Goyon Bayan Arewa Ba – Baba Ahmed
Published: 26th, April 2025 GMT
Ya koka kan halin da kasar ke ciki, kuma ya bukaci ‘yan arewa da su yi taka-tsantsan da ‘yan siyasa masu rarraba kawunan mutane da yaudara, gabanin babban zabe mai zuwa.
“Muna son gwamnati da za ta fahimci matsalolinmu kuma ta magance su. Bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari, mun dauki darasi.
”Yanzu haka muna cikin wata gwamnati, kuma har yanzu muna kuka. Kuka kadai ne muka san yadda za mu yi?” Baba-Ahmed ya tambaya.
Baba-Ahmed ya ce arewa ta sha wahala sosai a lokacin Boko Haram, wanda ya shafi dukkan kungiyoyi, ciki har da Musulmi da Kiristoci da Fulani da Baju, da sauransu, yana mai jaddada bukatar hadin kai.
“Kafin Buhari ya zama shugaban kasa, Boko Haram na kai hari kan masallatai, coci-coci, Abuja da Legas. Wannan shi ne lokacin da ‘yan arewa suka hada kai.”
Ya yi gargadi game rashin girmama yankin arewa, yana mai cewa ci gaba da rashin girmama yankin zai haifar da mummunan sakamako.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tallafa Wa Al’umma: Ya Dace Gwamnoni Su Yi Koyi Da Jihar Zamfara – UNDP
Sanarwar ta ƙara da cewa, ’yan kasuwa 1,000 za su samu jarin fara aiki na Naira 150,000 kowannensu, da nufin sauya akalar kasuwancin su zuwa sana’o’i na zamani a faɗin Jihar Zamfara.
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shiryen ƙarfafawa da dama tare da samar da damarmaki don cimma manufofinsa na ceto.
“Waɗannan tsare-tsare ba wani kebantaccen abu ba ne, wani ɓangare ne na babban burinmu wajen samar da jihar Zamfara mai albarka don haɗa abokan hulɗa don magance ɗimbim matsalolin zamantakewa da tattalin arziki.
“Yawancin tsare-tsare na rage raɗaɗin talauci da wannan gwamnati ta bullo da su sun yi tasiri ga rayuwar dubban ‘yan jihar, ƙudirin gwamnatinmu na kawar da raɗaɗin talauci yana haifar da ɗa mai ido. Za mu ci gaba da yin haɗin gwiwa tare da UNDP da sauran ƙungiyoyin masu ba da tallafi don samar da ɗorewar hanyoyi don fitar da mutanenmu daga ƙangin talauci.
“Tun da aka fara wannan shirin na bayyana cewa akwai tsari wajen zabi na gaskiya na waɗanda za su ci gajiyar shirin, don haka an zabo waɗanda suka amfana daga garuruwa da ƙauyuka kamar Sankalawa, Furfuri, Karal, Gusau, da Bungudu.
“Ina yawan nanata cewa ƙarfafa tattalin arziki dole ne ya kasance cikin haɗin kai a ƙarƙashin mu, ba tare da barin al’umma a baya ba, shi ya sa na dage wajen ganin an rarraba damarmaki cikin adalci a dukkan ƙananan hukumomin.
“Hakazalika, an gudanar da shirye-shiryen horarwa ga duk waɗanda suka ci gajiyar noman rani. Mun yi imani da cewa samar da albarkatu ba tare da ilimin yadda za a yi amfani da su ba, zai iya iyakance tasirin da shirin ke son cimma.”
Gwamna Lawal ya kuma miƙa godiyarsa ga Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan yadda suka amince da manufofin gwamnatinsa na ci gaba. “Ga waɗanda suka ci gajiyar, ina ba ku umarni da ku yi amfani da waɗannan albarkatun bisa ga gaskiya, kar ku ba ni kunya a kan yardar da nake da ita akan ku.
“Da waɗannan kalamai, abin farin ciki ne na a hukumance na ƙaddamar da rabon kayayyakin noman rani ga masu cin gajiyar 300 tare da raba jarin fara aikin na N150,000.00 ga ‘yan kasuwa 1,000.”
Tun da farko, shugaban ofishin UNDP na Arewa maso Yammacin Nijeriya, Ashraf Usman, ya bayyana cewa tasiri, sha’awa, da azamar gwamnatin jihar Zamfara a bayyane yake ga kowa da kowa, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga haɗin gwiwar.
“Na gode Mai girma Gwamna, waɗannan su ne dalilan da suka sa muka zo nan, ina taya ku murna da goyon bayan ɗimbin jama’a, na gode da irin misalin da ka ke bai wa sauran gwamnatocin jihohi wajen samar wa al’umma tallafi. Na gode da irin jagorancin ka.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp