Gaza: Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Asabar
Published: 26th, April 2025 GMT
Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama.
Mutane 4 sun yi shahada a harin na jiragen ‘yan sahayoniyar akan wani gida dake unguwar “al-Sabrah’ a kudancin birnin Gaza.
Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wani harin da asubahin yau Asabar akan wani gidan da yake a sansanin ‘yan hijira da “Mukhayyam-Shati’i.
Majiyar Falasdinawa ta kuma ambaci cewa, da asubahin yau Asabar sojojin HKI sun tarwatsa wasu gidaje a yankunan da suke gabashin birnin Kudus.
Dama a jiya Juma’a jiragen yakin HKI sun kai hari akan wata makaranta da take kunshe da ‘yan hijira na Yarmuk dake tsakiyar birnin Gaza wanda shi ma ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3.
A tsakiyar yankin na Gaza kuwa, manyan bindigogin HKI sun kai hare-hare a gabashin sansanin ‘al-Nusairat”.
A jiya kadai, Falasdinawa 48 ne su ka yi shahada a wasu hare-hare biyu da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa gidaje biyu a yankunan “Murtaji” da “al-fakhari” dake cikin garin “Khan-Yunusu” a kudancin zirin Gaza.
A efe daya, sojojin HKI suna ci gaba da tilastawa Falasdinawan yin hijira daga yankunan “Turkiman, da Jadid da suke a Arewacin unguwar Zaytun.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Tawayen Sudan Sun Kashe Fararen Hula 47 A Birnin El-Fasher Fadar Mulkin Darfur Ta Arewa
Mutane 47 ne suka rasa rayukansu tare da jikkatan wasu da dama a harin da aka kai da jirgin sama kan birnin El-Fasher na kasar Sudan
Runduna ta 6 da ke yankin El- Fasher ta sanar da mutuwar fararen hula 47 tare da jikkata wasu da dama sakamakon kazamin lugudan wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi kan birnin El- Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces na ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, inda suka yi amfani da harsasai masu yawa a yayin da suka yi ruwan wuta a kan unguwannin birnin El-Fasher a wannan mako, inda suka kashe fararen hula 47, ciki har da mata 10, wadanda hudu daga cikinsu sun kone a cikin gidajensu. Sannan an kashe mata hudu a wani bangare, yayin da mata biyu an kashe sune a lokacin da suke tafiya.