Mazauna Ƙauyen Batakashi da ke ƙaramar hukumar Garki a Jihar Jigawa sun yaba wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa tallafin abinci da ta kai musu.

Wasu daga cikin mazaunan da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu kan wannan karamci, tare da fatan alheri ga gidauniyar.

Daya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Malam Umar Abdullahi, ya ce gidauniyar ta kawo sassauci ga al’umma bayan iftila’in gobara da ya cinye gidaje kusan 45 a kwanan nan.

Haka shi ma Malam Usman Auwal,  ya nuna farin cikinsa, inda ya yaba da gwamnatin jihar Jigawa da kuma Gidauniyar Dangote, bisa tallafinsu ga al’umma.

A jawabinsa yayin kaddamar da rabon tallafin na buhunan shinkafa guda 500 masu nauyin kilogiram10, Shugaban ƙaramar hukumar Garki, Alhaji Adamu Kore, ya gode wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa ƙoƙarinta wajen taimakawa al’umma masu rauni a wannan lokaci da suke cikin bukatar.

Ya bayyana cewa wannan tallafi zai rage wa jama’ar ƙauyen Batakashi raɗaɗin halin da suka shiga sakamakon gobarar.

“Muna matuƙar farin ciki da tallafin Dangote da na gwamnatin jihar Jigawa, domin wannan gudummawa ta faranta ran daruruwan iyalai ba kawai a Jigawa ba har da sauran sassan ƙasar nan gaba ɗaya,” in ji Kore.

A nasa jawabin, Mukaddashin Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Alhaji Muhammad Murtala, ya ce Gidauniyar Dangote ta kawo buhunan shinkafa 40,000 masu nauyin kilo 10, domin rabawa talakawa da mabukata.

Maiunguwa, wanda kuma shi ne Daraktan Harkokin Gudanarwa da Kuɗi na hukumar, ya ce a ƙarƙashin gwamnatin Namadi, hukumar ta raba tallafi ga al’ummomi da iftila’i ko matsanancin talauci ya shafa.

Wakilin Gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Mustapha Umar, ya ce gidauniyar tana ba da tallafi ga al’ummomi a faɗin Najeriya domin rage wa marasa ƙarfi raɗaɗi.

Ya ce, “Dangote na shirye koyaushe ya taimaka wa ‘yan Najeriya ta hannun Gidauniyar Aliko Dangote, wadda aka ƙirƙira domin aiwatar da ayyukan jinƙai.”

Radio Nigeria ya ruwaito cewa Gidauniyar ta bayar da buhunan shinkafa 500 masu kilo 10 da tabarma 100 ga al’ummar Batakashi da ke yankin Garki a jihar Jigawa, waɗanda gobara ta shafa.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa ce ta jagoranci aikin rabon kayan tallafin.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gidauniyar Dangote Jigawa Gidauniyar Aliko Dangote

এছাড়াও পড়ুন:

Yayin Da Ake Fuskantar Daminar Bana: Sabbin Hare-hare Na Barazana Ga Shirin Wadata Kasa Da Abinci

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rashin Wutar Lantarki: Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa Na Samun Wutar Awa 2 Ne Kacal A Kullum
  • Jigawa Ta Bude Sabon Babi: Maniyyata Za Su San Masaukansu Tun Daga Gida Najeriya
  • Sojonin Yemen Ta Kakkabo Jiragen Yakin Amurka Wadanda Kimarsu Ya Dalar Amurka Miliyon $200 A Makonni 6
  • Yayin Da Ake Fuskantar Daminar Bana: Sabbin Hare-hare Na Barazana Ga Shirin Wadata Kasa Da Abinci
  • **Gwamnati Za Ta Kwace Gidajen Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya Ba Su Biya Bashin Gidaje Ba
  • Gwamnatin Kano Da NBC Sun Shirya Taron Bita Domin Tsaftace Harkar Siyasa
  • Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
  •  Ghana Ta Fada Cikin Takaddama Bayan Tisge Babbar Mai Shari’a Ta Kasar Da Shugaban Kasa Ya Yi
  •  WHO: Masu Ciwon Koda 400 A Gaza Sun Mutu Saboda Rashin Magani