HausaTv:
2025-04-26@17:03:38 GMT

Iran Ta Gabatar Da Tayin Shiga Tsakanin Don Sasanta Indiya Da Pakisatan

Published: 26th, April 2025 GMT

A dai-dai lokacinda kasashen Indiya da Pakisatn suke tada jijiyoyin wuta kan wani harin ta’addanci da ya kai ga mutuwar mutane 27 masu yawon shakatawa a yankin Kashmir na kasar Indiya, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gabatar da tayin shiga tsakani don dai-daita tsakanin kasashen biy.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka, a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa Iran tana da dangantaka mai karfi tsakaninta da kasashen biyu, kuma makobta ne kuma yan uwa wadanda suke da tsohuwar dangantaka ta al-adu a tsakaninsu na karnuka, ba za muyi kasa a guiwa wajen sasantasu ba, idan sun bamu wannan damar.

A cikin makon da ya gabata ne wasu yan bindiga suka bude wuta kan wasu maso yawan shakatawa a yankin Kashmir na kasar Iran inda mutane 27 suka mutu. Gwamnatin Undiya tana zargin Pakistan da hannu dumu-dumu a cikinsa, a yayinda gwamnatin kasar Pakisatan ta musanta hakan ta kuma yi allawadai da harin. Amma ta kara da cewa idan indiya ta kuskura ta yi amfani da makami a kanta to zata rana.

A daren jamm’an da ta gabata dai bangarorin biyu sun kai ga musayar wuta a tsakaninsu a kan iyakokin kasashen biyu.

Ministan ya bayyana cewa kasar zata yi amfani da ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Islamabad da kuma New Delhi don shiga tsakanin  su idan sun amince da hakan.

Kasashen indiya da Pakistan dai sun dade suna takaddama kan mallakar Yankin Kashmir kuma sun sha shiga yaki saboda hakan.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Yanzu Ne Lokacin Da Arsenal Ya Kamata Ta Lashe Kofin Zakarun Turai – Walcott

Karo na hudu kenan da Arsenal ta kara da Real a kofin Zakarun Turai, inda ta ci uku aka yi canjaras daya. A ranar 29 ga watan Afrilu Arsenal za ta karbi bakuncin PSG a wasan farko, kafin a buga na biyu mako daya bayan haka. Kungiyar dai ita ce a mataki na biyu a kan teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila inda a wannan satin ake saran Liberpool za ta zama zakara a bana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rasha Ta Fara Aika Isakar Gas Zuwa Kasar  Iran Ta Azarbaijan Don Sayarwa A Kasuwannin Duniya
  • Yanzu Ne Lokacin Da Arsenal Ya Kamata Ta Lashe Kofin Zakarun Turai – Walcott
  • Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya
  • Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasarsa A Shirye Take Ta Sulhunta Tsakanin Pakistan Da Indiya
  • Duniyarmu A Yau: Shiri Kasashen Yamma Na Kashe Dukkan Falasdinwa A Gaza
  • Sin Ta Musanta Yin Shawarwari Ko Tattaunawa Da Amurka Kan Batun Harajin Kwastam
  • Sin Ta Ce Ya Kamata Amurka Ta Tattauna Da Ita Bisa Mutuntawa Matukar Da Gaske Take
  • Arakci: Mun Yi Tattaunawa Mai Kyau Da Mahukuntan Kasar China