Bayan Shekaru 10 Madrid Da Barcelona Zasu Sake Yaɗuwa A Wasan Ƙarshe Na Copa Del Rey
Published: 26th, April 2025 GMT
Manyan kungiyoyin kwallon kafa Barcelona da Real Madrid zasu sake haduwa a wasan da ake yima kallon wasa mafi kayatarwa da akeyi a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a halin yanzu.
Manyan kungiyoyin biyu duka na da dadadden tarihin iya taka leda da nuna kwarewa a harkar kwallon kafa, nasarorin da suka samu a kwallo ya sa ana yimasu kallon gagarabadau kokuma ace daukakakkun kungiyoyin kwallon kafa a Duniya.
Yau Asabar Barcelona da Real Madrid zasu buga wasan karshe na kofin Copa Del Rey a filin wasa na De La Cartuja dake birnin Sevilla, Barcelona ta doke Athletico Madrid da ci 5-4 a wasanni biyu da suka buga kafin ta kawo wannan matsayi.
Hakazalika Real Madrid ta fitar da Real Sociedad a wasan na kusa da na karshe da ci 5-4 a wasanni biyu da suka buga tsakaninsu, alkalin wasa Ricardo De Burgos Bengoatxea ne zai jagoranci wasan duk da rashin yarda da Real Madrid ta nuna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kwallon kafa
এছাড়াও পড়ুন:
Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja
Wani matashi mai shekaru 30 ya kashe kansa bisa rahotanni bayan rasuwar ƙaramar matarsa a ƙauyen Ikumi da ke Ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja.
Majiyoyi sun bayyana cewa magidancin mai mata biyu ya sha fama da matsalolin tunani da na zuciya tun bayan rasuwar matarsa ta biyu a watan Maris na wannan shekara.
Sun ƙara cewa ya kasance yana yawan bayyana cewa ba zai iya samun kwanciyar hankali ba tare da marigayiyar ba.
Shaidu sun bayyana cewa ya yi amfani da bindigarsa ta toka wacce yake farauta da ita wajen harbe kansa har lahira a gonarsa.
Wata majiya ta ce ya bar matarshi ta farko da manya da kuma yara biyu. Kakakin ’yan sanda a Jihar Nijar, SP Wasiu Abiodun, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 24 ga Afrilu, 2025.
’Yan kasuwar da suka ɓoye kayan abinci na tafka asara Na shiga fim ne don isar da saƙon Musulunci — Malam Inuwa Ilyasu ’Yar Arewa da ta kafa tarihin samun Digiri Mai Daraja ta ɗaya a fannin Shari’aA cewarsa, “A ranar 24 ga Afrilu, 2025 da misalin ƙarfe 8 na dare, an samu rahoto cewa wani Stephen Moses mai shekaru 30 daga ƙauyen Ikumi ta yankin Shako na ƙaramar hukumar Gawu-Babangida, ya harbe kansa a kirji da bindiga a gonarsa da rana.
“Jami’an ’yan sanda na Gawu-Babangida sun ziyarci wurin da abin ya faru, sun samu bindiga da kuma gawar a ƙasa, an kai gawar asibiti yayin da bincike na farko ya nuna cewa mamacin yana cikin zaman makokin rasuwar matarsa wacce ta rasu kwanan nan, kuma ya kasance yana barazanar kashe kansa, amma ’yan uwansa ba su sanar da ’yan sanda ba don ɗaukar matakan kariya.”