Aminiya:
2025-04-26@23:13:09 GMT

An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji

Published: 26th, April 2025 GMT

Iyalan wata dattijuwa da suka nema suka rasa sun shiga fargaba bayan gano gawarta a cikin wani maciji.

Lamarin na zuwa ne bayan kumburin ciki ya bayyana sosai a kasurgumin maciji — kafin dangin tsohuwar su gano cewa maciji ya haɗiye kakarsu a cikinsa.

Sojoji sun kashe ’yan ta’dda 1,770 sun kama 3,070 a Arewa —Janar Musa Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja 

Iyalan matar da ta ɓace sun bi sawun macijin zuwa wani mai yawan ciyayi a kudancin Sulawesi na kasar Indonesia.

’Yan yankin sun tsorata matuka lokacin da suka ga maciji mai tsawon kafa 26 ya yi nauyi da wani babban kumburi a cikinsa.

A lokacin da suka farka cikin macijin, sun gano gawar matar mai suna Hasia mai shekara 66, wadda ta bata a lokacin da take komawa gida daga wurin aikinta a wata gonar roba.

Ana kyautata zaton macijin ya fito ne daga dogayen ciyayin ya sari kafarta, wanda hakan ya sa ta faɗi.

Ɗan matar mai suna Nurdin, ya ce danginsa da ke cikin damuwa, sun kaddamar da bincike lokacin da dare ya yi, bayan da suka lura tsohuwar ba ta dawo gida ba.

Sun yi cigiya kafin su far wa macijin da misalin ƙarfe 9 na dare.

Sai suka sari macijin, suka buɗe cikinsa, inda suka tarar da gawar Hasia a cikinsa.

Nurdin ya razana, inda ya ce: ‘Wannan abu ne mai ban tsoro.

“Na san mutuwa ce mai raɗaɗi ga mahaifiyata, kodayake macijin ya mutu.

“Ba zai taɓa dawo da ita ba. Yanzu muna addu’ar Allah Ya jikan ta da rahama.

Ipda Zakaria, Shugaban ‘yan sandan PituRiase, ya ce: ‘Yanzu haka, ana shirin yi wa matar jana’iza.’

“Saboda haka, muna kira ga mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan wajen tafiya, domin an san cewa akwai manyan macizai a dajin.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: dattijuwa Tsohuwa

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe Shugaban coci da wata mace a Benuwe

A wani sabon tashin hankali ya yi sanadiyyar rasa  rayukan wani shugaban cocin Roman Katolika da wata mata a ƙauyen Ayua da ke gundumar Mbayer/Yandev a ƙaramar hukumar Guma a Jihar Benuwe.

Shedun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, lamarin da ya sa mazauna yankin da ke kewayen yankin Mbagwen da ke ƙaramar hukumar Guma ƙaurace wa gidajensu sakamakon hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa.

An sako limamin Katolika da aka sace a Kaduna An kama mutum 2 ɗauke da ƙwayar tramadol ta N150m a Kano

Waɗanda aka kashen dai sun haɗa da: David Hur, shugaban shiyyar Cocin Anter Catholic da Misis Lydia Utuu ta ƙauyen Ayua.

Majiyoyi sun yi zargin cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon wata arangama tsakanin wani makiyayi da wani mazaunin ƙauyen.

Rahotanni sun ce makiyayin ya yi yunƙurin wanke kansa ne a wata hanyar ruwa ɗaya tilo da al’umma ke da shi bayan ya sha daga ciki. Wani ɗan unguwar ya nuna rashin amincewarsa, wanda hakan ya haifar da rikici inda ake zargin makiyayin ya kai masa farmaki da adda.

“Mutumin ya yi neman agaji don jawo mutanen ƙauyen zuwa wurin, amma hargitsin ya kaure da sauri zuwa wani mummunan yanayi,” kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, mazauna yankin sun bar gidajensu da yawa. Har yanzu dai ana zaman ɗar-ɗar, tare da yin kira ga gwamnati da jami’an tsaro su shiga tsakani domin daƙile ci gaba da zubar da jini.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe, CSP Catherine Anene ba ta amsa tambayoyi kan lamarin ba don ƙarin haske a lokacin haɗa wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Damfarar CBEX: Mutum 8 da EFCC ke nema ruwa a jallo
  • Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina  Cikin Masifar Yunwa
  • An Gano Naira Miliyan 27.8 Da Suke Zirarewa A Albashin Kano
  • Gwamnatin Kano Ta Gano  An Biya Wasu Ma’aikatan Bogi Naira Miliyoyi
  • An kashe Shugaban coci da wata mace a Benuwe
  • An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi
  • An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure
  • **Gwamnati Za Ta Kwace Gidajen Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya Ba Su Biya Bashin Gidaje Ba
  • Congo Da M23 Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta