Tashin Gobara A Tashar Jirgi Ruwa Na Shahid Raja’i Da Ke Kudancin Iran Ya Jikkata Mutane Masu Yawa
Published: 26th, April 2025 GMT
Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran
Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu.
A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu.
Fashewar ta yi karfi sosai, ta yadda mazauna Bandar Abbas da Qeshm suma suka ji karar fashewar.
Daga baya an bayyana cewa lamarin ya faru ne sakamakon fashewar tankar mai a tashar ba tare da sanin wani dalili ba, kuma nan take aka aike da tawagogin ma’aikatar bada agajin gaggawa zuwa yankin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shahid Raja
এছাড়াও পড়ুন:
Sojan HKI Ya Halaka A Gaza
Kafafen watsa labarun HKi sun amabci cewa daya daga cikin sojojinsu ya halaka a Gaza, yayin da wasu 7 su ka jikkata.
Kafafen watsa labarun na HKI sun ce, Harin da aka kai wa sojojin ya kunshi harbi daga kwararren maharbi da kuma harba makamin dake fasa motoci masu sulke.
An ga jiragen sojan mamaya suna tsananta hare-hare a yankin da lamarin ya faru, saboda su sami damar dauki gawar sojan nasu da kuma wadanda su ka jikkata.
Tashar talabijin ta 12; ta HKI ta ambaci cewa;Ana gwabza fada ne a arewacin Gaza, kuma mazauna yankin suna cewa sun ga jiragen sama masu yawa suna kai da komo.
Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare masu yawa a yankin Arewacin Gaza, kamar kuma yadda wata kafar ta ce an ji karar fashewar wasu abubuwa da karfi a cikin yankin Naqab ta yamma.
A wani labarin daga Gaza, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a yau kadai sun kai 56.
Jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a yankunan Arewan yammacin Gaza da kuma Jabaliya da shi ne musabbabin shahadar adadi mai yaw ana Falasdinawan a yau.
A Jabaliya kadai jiragen yakin HKI sun kai hari ne akan wani gida da ‘yan hijira suke cikinsa, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 15.
A Arewacin Gaza kuwa mutane an sami shahidai 39, sai kuma wasu 7 da su ka jikkata a cikin birnin Gaza kamar yadda kamfanin dillancin labarun “Anatoli” ta Turkiya ya nakalto.