Aminiya:
2025-04-27@04:04:02 GMT

Abubuwan da suka faru yayin jana’izar Fafaroma Francis

Published: 27th, April 2025 GMT

Dubun dubatar mutane mabiya Addinin Kirista ne suka yi cikar ƙwari a jana’izar ƙarshe da ake yi wa jagoran ɗarikar Katolika, Fafaroma Francis, a cikin yanayi na matakan tsaro.

Hukumomi a birnin Roma sun tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen St. Peter’s Square na Fadar Vatican, inda ake gudanar da jana’izar Fararoma Francis.

Damfarar CBEX: Mutum 8 da EFCC ke nema ruwa a jallo An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji

Tun da sanyin safiya dubun dubatar jama’a suka yi wa dandalin cikar ƙwari domin samun damar yi wa Fafaroma Francis ganin ƙarshen a jana’izar da ke zama guda a cikin mafi girma a duniya.

Mutum dubu 400 sun halarci jana’izar

Aƙalla mutum 400,000 ne suka halarci jana’izar Fafaroma Francis a dandalin St Peter’s da ke Vatican.

Haka kuma sun ga lokacin da aka ɗauki gawarsa zuwa wajen da aka binne shi a cocin Santa Maria, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gidan Italiya.

“Mun yi ƙiyasi cewa mutane 400,000 ne tsakanin waɗanda suka halarci dandalin St Peter’s da kuma waɗanda suka tsaya kan tituna suka kalli jana’izar,” in ji Matteo Piantedosi.

Shugabannin duniya da suka halarci jana’izar

Shugabannin manyan kasashen duniya ciki har da na Faransa da Amurka da wasu jagororin gwamnatoci ciki har da na Jamus da Burtaniya da fitattun sarakunan duniya irinsu na Jordan, duk sun halarci jana’izar.

Shugaba Putin bai samu halartar jana’izar ba, amma kuma takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ya halarta dandalin na St. Peter’s don yi wa Fafaroma Francis ganin karshe.

Daga cikin fitattu a dandalin St Peter da safiyar ranar Asabar akwai Yarima William na Birtaniya da shugaban Amurka Donald Trump da wanda ya gada, Joe Biden da Firaiministan Birtaniya, Sir Keir Starmer da kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Jana’izar na zuwa ne bayan kammala yi wa gawar Fafaroma ganin bankwana na tsawon kwanaki da wasu dubban mabiya ɗarikar ta Katolika suka yi a cikin yanayi na juyayi da alhini.

Fafaroma na farko da aka binne a wajen Vatican cikin shekaru 100

Fadar Vatican ta tabbatar da cewa an binne Fafaroma Francis a cocin Santa Maria Maggiore.

“Fafaroma Francis shi ne mutum na farko cikin shekara 100 da aka binne a wajen Vatican, kuma an binne shi a asirce, inda makusantansa suka yi masa gaisuwar ban-girma,” a cewar sanarwar da fadar ta fitar.

Shi ne Fafaroma na farko tun bayan Leo XIII, wanda ya mutu a 1903 — da aka a binne a wajen Vatican.

Kowane lokaci idan ya koma birnin Rome daga balaguro, ya sha ziyartar Santa Maria Maggiore.

Cocin dai yana wajen Vatican da ke tsakiyar birnin Rome.

Mutumin farko daga Latin Amurka da ya zama Fafaroma

Ɗan ƙasar Argentina, wanda ya yi jagorancin majami’ar Katolika tsawon shekaru 12, ya mutu ne a ranar Litinin da ta gabata yana da shekaru 88, bayan fama da mutuwar ɓarin jiki da bugun zuciya.

Kiraye-kirayen zaman lafiya

Francis ya sha yin kiraye-kirayen kawo ƙarshen rikice-rikicen duniya a zamanin jagorancinsa, kuma jana’izarsa ta bai wa shugaba Trump na Amurka, wanda yake koƙarin kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine damar ganawa da takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelenskiy a cikin majami’ar Saint Peter Basilica.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Fadar Vatican Fafaroma Francis halarci jana izar Fafaroma Francis a wajen Vatican a jana izar

এছাড়াও পড়ুন:

Yayin Da Ake Fuskantar Daminar Bana: Sabbin Hare-hare Na Barazana Ga Shirin Wadata Kasa Da Abinci

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno
  • Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasarsa A Shirye Take Ta Sulhunta Tsakanin Pakistan Da Indiya
  • Yayin Da Ake Fuskantar Daminar Bana: Sabbin Hare-hare Na Barazana Ga Shirin Wadata Kasa Da Abinci
  • Sin Da Kenya Sun Daukaka Dangantakarsu Yayin Da Xi Da Ruto Suka Gana
  • Kasar Yemen Zata Aiwatar Da Abubuwan Mamaki Da Zasu Firgita Makiyanta Kuma Abokan Gaba
  • Tallafa Wa Al’umma: Ya Dace Gwamnoni Su Yi Koyi Da Jihar Zamfara – UNDP
  • NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci