Muhimman Dalilan Kirkiro Da Shirin Inganta Aikin Noma ‘SAPZ’
Published: 27th, April 2025 GMT
Kazalika, a cikin daukacin gwamnatin tarayya da kuma na jihohin kasar, an tsara yadda za su dakile kalubalen da fannin aikin noma da kuma yadda za a sama wa manoman kasar sauki, bunkasa rayuwar mazauna karkara da kuma habaka tattalin arzikin kasar.
Akasarin manufar aikin na SAPZ shi ne, domin inganta aikin noma a karkara, maimakon fitar da amfanin gona kamar irin su Rogo, Shinkafa, Tumatir da kuma Koko zuwa birane ko kuma kasar waje, za a tanadar da kayan aiki a yankunan da aka tsara za su amfana da shirin, domin manoman yankin su samu ribar da ta kamata.
Daya daga cikin manyan matsalolin da ake samu a Nijeriya ita ce, gibin da ake samu a bangaren aikin noma domin samun riba.
Amma a wadannan yankunan da za a gudanar da aikin, za a samar da masana’antun sarrafa amfanin gona, kayan adana amfanin gona, wutar lantarki mai dorewa, tituna da kuma cibiyoyin bayar da horo.
Nijeriya dai, ta shafe shekaru tana fama da karancin abinci, asarar da manoma ke tabkawa bayan sun yi girbi da kuma matsalar rashin aikin yi a tsanakin ‘yan kasar.
Har ila yau, aikin zai kuma samar da damar fitar da amfanin gona zuwa ketare, wanda hakan zai samar wa da Nijeriya biloyin Nairori.
Ta hanyar aikin na SAPZ, Nijeriya za ta iya samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, rage asarar da ake fuskanta duk shekara, bayan girbe amfanin gona da kudinsu ya kai kimanin Naira tiriliyan 3.5, samar da ingantacce wajen adana amfanin gona, samar da cibiyoyin bayar da horo ga manoma da kuma cike gibin da ake da shi a kasuwannin kasar.
Kashi na farko na aikin, an kaddamar da shi ne, a 2022, ta hanyar ware dala miliyan 538, wanda kuma za a wanzar da shi a cikin akalla sama da shekaru biyar.
Aikin na Bankin AfDB, zai samar da dala miliyan 210, inda kuma Bankin IsDB da IFAD, za su samar da dala miliyan 310, sai kuma gwamnatin tarayya da za ta samar da dala miliyan 18.05.
Jihohin Da Za Su Amfana Da Aikin:
Jihon da za su amfana da aikin su ne; Kaduna, Kano, Kwara, Kuros Riba, Imo, Ogun, Oyo, sai kuma Abuja.
A yanzu dai, Shugaban Bankin AfDB, Akinwunmi Adesina da kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ne, ke jagorantar aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: dala miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Nazari Kan Amfanin Noman Kanumfari
Manomin da zai shuka Irin noman Kanumfari, ana bukatar ya sa hakuri, idan har kana bai wa Bishiyarsa kulawar da ta dace, za ta iya shafe tsawon shekara 100 ko sama da haka.
Ana bukatar wanda zai shuka shi, ya tabbatar ya shuka Irin noman a kasar noma mai inganci, sannan kuma yana daukar dogon lokaci kafin ya kammala girma.
3. Ba Shi Kulawar Da Ta Kamata:
Ana iya shuka Irin noman Kanumfari a gida, kuma zai iya yin girma; amma ya fi bukatar yanayin da yake da zafi, haka nan ko da an shuka shi a yanayin da ya dace, yana kai wa tsawon shekara bakwai kafin ya kammala girma, kazalika, ana bukatar wanda ya shuka Irin noman, ya tabbatar da amfanin na samun hasken rana a kullum, har Ila yau, iska mai karfi na yi wa Bishiyarsa illa, musamman a lokacin da take tasowa.
4. Ba a son wanda zai shuka Irin nomansa, ya shuka wanda ya bushe, domin matukar aka bar Irin ya bushe, ba zai taba girma ba.
5. Ba a son wanda zai noma shi, ya bar Irin a cikin rana, ana bukatar ya samar masa wajen da ya fi da cewa tare da yi masa ban-ruwa akai-akwai, haka nan, ana so a bar Irin ya girma har zuwa wata shida, bayan an shuka shi kafin a canza masa wajen da za a sake shuka shi, haka yawan yi masa ban-ruwa na iya jawo mutuwar Irin da aka shuka shi.
6. Ana son Irin nomansa da aka shuka, akalla ya kai daga wata 18 zuwa wata 24, kafin a canza masa wani wajen, haka Irin nomansa na girma ne a hankali, amma ana bukatar Irin ya kasance ya yi karfi sosai, don ya samu sukunin dorewarsa, musamman idan an shuka Irin a fili.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp