Aminiya:
2025-04-27@15:42:30 GMT

Sulhu da ’yan bindigar Katsina: Gaba aka ci ko baya?

Published: 27th, April 2025 GMT

Sama da kwanaki hamsin da suka shuɗe ne aka aiwatar da sasanci a tsakanin wasu ’yan bindigar daji da al’ummomin da suka addaba don ganin an samu zaman lafiya a tsakanin yankunan.

Sasancin, rahotannin da muka samu sun ce, jami’an tsaron Gwamnatin Tarayya ne suka shirya tare da tsara yadda za a yi shi karkashin kulawar sojoji.

Kazalika, mun samu rahoton cewa, su ’yan ta’addan ne suka nemi a yi sulhun, sabanin baya inda aka neme su da yin hakan har sau biyu a lokacin mulkin tsohon Gwamna Aminu Bello Masari, amma babu wanda yake daukar wani lokaci yake wargaje.

Gwamna Radda ya tubure

Duk da cewa, har zuwa rubuta wannan rahoto, Gwamna Dikko Radda yana nan kan bakansa na cewa babu shi babu neman yin sasanci da dan ta’adda sai fa idan shi dan ta’addan ne ya nema kuma ya tabbatar da hakan tare da kiyaye dokokin da za a gindaya.

Kafin sasancin yankin Karamar Hukumar Batsari, wanda su jami’an suka jagoranci yi, a can wasu yankuna na Karamar Hukumar Faskari musamman sashen da ɗan bindigar nan Adamu Aliero ke gudanar da harkokinsa, mun samu labarin an samu irin wannan sasanci a yankuna irin su Birnin Kogo da kewaye.

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi mu boye sunansa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, “shi da kansa Alieron ya ba mu wannan tabbaci na cewa mu dawo gidajenmu da gonakinmu mu gyara.

“Kuma ya ce lallai ba zai bari wata daba ta zo ta cuce mu.”

Sulhun Batsari

A yankin Karamar Hukumar Batsari aka fara gudanar da wannan sasanci karkashin kulawar Laftanar-Kanar Aminu na Bataliya ta 17 da ke Jihar ta Katsina yayin da Abu Radde ya jagoranci bangaren ’yan bindigar.

Zuwa lokacin da muke rubuta wannan rahoto, tabbatattun rahotanni sun ce, tun daga da aka yi zaman sasancin a wani kauye mai suna Kofa sama da kwanaki hamsi da suka shude, ba a kara kai hari ba a karamar hukumar.

Kazalika, hanyar da ta tashi daga Katsina zuwa Batsari babu wata matsala kuma ana iya tafiya komin dare.

Maganar daina kai hari da tsare hanya na daga cikin sharuddan wannan sasanci, inda a daya bangaren kuma, za a bar maharan za su rika shigowa cikin al’umma suna gudanar da hidimomin su kamar kowa.

Sasancin Jibiya

Bayan sasancin na Karamar Hukumar ta Batsari wanda babu sa hannun gwamnatin jiha a cikinsa, sai kuma na yankin Karamar Hukumar Jibiya, wanda shi ma Laftanar-Kanar Aminu ne ya jagoranci jami’an tsaro, a daya bangaren kuma Audu Lankai ya jagoranci ’yan bindigar daji.

Sabanin na yankin na Batsari, a yankin na Jibiya an dan samu turjiya daga wasu manyan ’yan bindiga, Bala Wuta da Aloda da Alo da suka nuna kin amincwar wannan tsari na sasanci.

A satin farko bayan yin sasancin Bala Wuta da tawagarsa suka tare hanyar Jibiya zuwa Batsari, inda wasu rahotannin suka ce har ma sun tafi da wasu mutane.

Amma shi jagoran sasancin Audu Lankai ya bi har garin su shi Bala, ya yi masa dukan kawo wuka, aka kuma ci shi tarar kudi naira milyan uku.

To daga baya an ce shi ya bi, amma dai sama-sama.

Sai kuma shi Aloda wanda aka ruwaito cewa dan-uwa ga shi Wuta ne, shi da yaransa suka shigo har yankin Magamar Jibiya suka kora wasu dabbobi, amma da aka shaida wa shi Lankai kamar yadda yake cikin yarjejeniyar da cewa, duk wanda ya yi wani laifi daga cikin mutanensu a gaya masu kuma a zura ido a ga irin hukuncin da zasu dauka; Ba tare da bata lokaci ba sai ga dabbobin an maido.

Har’ila yau, yaran su Aloda sun tare wata hanyar kauyuka suka amshe wa wasu kayan abincin da suka sayo da kudade da wayoyi.

A nan ma sai da suka maido duk abin da suka karba illa wayar, bayan jin karar wayar daga mai ita an ce shi Lankai ya biya kudin.

Har’ila yau, akwai wani mai suna Alo, wanda ake yi wa lakabi da Dan-ina da kisa, wanda har yanzu su Lankai din ke neman shi saboda ya gudu.

Su kansu su Bala Wuta da Alodan an ce sun shiga wasan buya saboda neman da shi Lankai ke yi masu kan kisan dan-uwansa da suka yi.

Mun samu labari, bayan yin sasancin ne Lankai ya tura kanensa ya karbo mishi bindigoginsa da ke wajensu, amma sai sa-insa ta shiga tsakaninsa da su kanan Balan, wanda ya harbe shi har lahira.

Wannan ya sa Lankai sake zuwa gidan Balan da ke Mazanya ya koro dabbobin Balan ciki har da rakumma, domin kafin ya je sun gudu.

Su kuma suka kai hari inda suka kona masa ma’ajiyarsa da ke Fafara. Wannan tataburza da ta shiga tsakaninsu ta ja hankalin mutane sosai.

Amma gab da kammala rubuta wannan rahoto mun samu labarin cewa an shiga tsakani domin sasantawa.

Har’ila yau, mun samu labarin cewa, a can ma yankin Zamfara, Bello Turji da Dankarami suna shirin yin wani zama tsakaninsu domin daukar irin wannan mataki na sulhu inda suke fatan hada guiwa da su Lankai don a tafi bai daya.

Akwai wani makamancin irin wannan rahoto na sasanci a yankuna Ruwan Godiya ta Karamar Hukumar Faskari da yankin Guga ta Karamar Hukumar Bakori da sauran wasu sassan.

Sai dai kananan hukumomin Dutsinma da Malunfashi da Kafur da Dandume da Sabuwa har yanzu ba su daina fuskantar wannan matsala ba.

Misali, a yankin Malumfashi kawai, ana kawo harin a gefen gari abin sai da ta kai har cikin garin.

Ba da jimawa an shiga an dauke wani dan kasuwa mai suna Alhaji Yahuza Malumfashi da kuma wani Ali Mai Gwanjo, wadanda sanannu ne a garin na Malumfashi.

Jama’a sun ɗauki matakain kare kansu

Alhaji Muhamma Garba MG, tsohon Mai Taimakawa Gwamna Masari ta Fuskar Sadarwa na Shiyyar Funtuwa kuma daya daga cikin ’yan kwamitin tsaro a yanki na Malumfashi ya shaida wa wakilinmu irin matakan da suke dauka a yanzu a lokacin tattaunawarsu ta wayar salula.

“Gaskiya rabon da a ce an ɗauki wani a wannan yankin tun lokacin da suka dauki Balan Auwalu a farkon azumin nan da ya wuce.

“Kwana biyar kafin Salla sun zo inda suka raba kansu kashi hudu da nufin afkawa garin amma jama’a suka nuna masu ba su isa ba.

“Haka aka yi ta zagayezagaye a wannan rana, in sun nufi nan a tare har dai suka gaji suka tafi. Gaskiya yanzu garin Malunfashi bai shiguwa.”

’Yan ta’adda sun sha da kyar

Alhaji MG ya kara da cewa, “Sun kuma je garin Ruwan Sanyi da nufin daukar wani mai hali, jama’ar garin sun yi amfani har da duwatsu wajen korar wadannan ’yan ta’adda.

“Duk da cewa, sun kashe wani sun raunata wasu amma hakkan bai sa jama’ar sun karaya ba.

“A lokacin ma har wata budurwa suka yi yunkurin tafiya da ita amma ta cije duk da jan ta a kasa da suka rika yi amma ba su tafi da ita ba.

“Da suka ga haka, sai suka nufi gidan wani Bafillace da nufin ya boye su amma rashin biya masu bukatar ta su nan take suka kashe shi.

“Sun dai sha da kyar. Akwai wata mata da suka sako ta zo tana bada labari cewa, ta ga irin yadda wani lokaci suka koma a fusace har ma suna jifa da bindigoginsu don haushin rashin samun damar shiga garin na Malumfashi,” Fulani sun shigo gari.

A yankunan da suka yi sasanci da ’yan bindigar suna nuna jin dadinsu a kan zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu.

Wani Bafilatani da wakilinmu ya tuntuba a kasuwar Jibiya ya ce, “Yanzu ga ni a cikin kasuwa ina yawo, ina sayen duk abin da nake so kuma ina gani kamar kyauta ake ba ni.

“Wannan lemun naira 400 na saya amma a cikin daji har 3,000 muke saye. Yanzu nan wajen aski zani, dubi kaina. Wannan wandon naira dubu biyar na saye shi. Daji babu irinsa,” in ji shi, amma bai yarda mu dauki hotonsa.

Wata Bafilata mai suna Hashe da muka samu tana sayen kayan kyalliya ta ce, “Yau shekara ta 12 ban shigo cikin gari ba balle in zo kasuwa.

“Muna cikin daji zaman babu dadi sai dai babu yadda zamu yi. Amma yanzu am! Ina jin dadi sosai. Ga ni a cikin kasuwa ina yawo babu wanda ya ce komai balle hankalina ya tashi.

“Can baya yaya za a yi in shigo cikin gari ma ba kasuwa ba? Gaskiya mutanen mu ba su kyauta ba. Muna zamanmu lafiya da Hausawa an zo ana so a raba mu.”

Shi ma wani Bafillacen wanda wakilinmu ya taras ana yi mashi gyaran babur, mun ji yana cewa, shi zai baro daji baki daya ya dawo cikin mutane. Ashe zaman kunci yake yi a dajin.

Ya ce “Mun ji yana cewa, mutun ya tara kudin kuma ya rasa yadda zai yi da su. Sai dai duk wadda zata faru ta faru amma birni zan dawo kuma yana fatan ya mutu a cikin mutane.”

Alhajin da ya lura wakilinmu yana sauraren hirarsu, sai ya yi murmushi ya ce, “Allah Malam, kara mutun ya baro waccan masifar ya dawo inda yake da walwala sosai, ya ci duk abin da yake so.

“Babu wanda ya damu da kai. Kai da kowa sai gaisuwar arziki.”

Sai dai wasu jama’ar da wakilin mu ya tuntuba akan tasirin wannan sasanci, suna nuna shakku matuka ganin irin yadda abin da ya faru a lokuttan baya.

Wasu kuwa cewa suka yi cewar, a dai ƙara zura ido har zuwa faduwar ruwan damina a ga abin da zai faru. Suna masu ra’ayin cewa, har dai aka yi noman bana lafiya, to lallai sulhu zai dore.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Dikko Umar Radda Jihar Katsina Karamar Hukumar wannan sasanci wannan rahoto yan bindigar irin wannan

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kashe ’yan ta’dda 1,770 sun kama 3,070 a Arewa —Janar Musa

Rundunar Sojin Najeriya ta samar da cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda 1,770, sun kama wasu 3,070 a yankin Arewa maso Yamma a shekaru uku da suka gabata.

Rundunar ta kuma yi nasarar ceto mutane fiye da 2,515 da harin ya rutsa da su ta hanyar gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a jihohin da lamarin ya shafa.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya sanar da hakan a yayin wani gangamin wayar da kan jama’a a Jihar Katsina, wanda aka gudanar ga mazauna ƙananan hukumomin Batsari da Dutsin-Ma.

Janar Musa ya ce, sun kuma ƙwato sama da makamai 1,000 da alburusai 12,000 a hare-haren da suka kai a jihohin Arewa maso Yamma guda biyar, wato Katsina, Kaduna, Kebbi, Sokoto, da Zamfara, tare da daƙile ayyukan ta’addanci.

Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja Janyewar sojoji ke ba Boko Haram damar ƙwace yankuna —Zulum

“Sojoji na yin iya ƙoƙarinsu wajen yaƙi da matsalar tsaro,” in ji shi, yana mai jaddada cewa nasarorin da aka samu wani ɓangare ne na ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.

Aikin na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar al’umma da shugabannin sojoji da mazauna yankuna a wani yunƙuri na ƙulla alaƙa mai ƙarfi da ƙarfafa sanya ido a tsakanin al’ummomi.

A yayin taron wayar da kan al’umma, Janar Musa ya tunatar da mazauna yankin cewa wanzar da zaman lafiya nauyi ne na haɗin gwiwa. Ya kuma yi kira ga al’ummomin da su ba da rahoton abubuwan da ake zargi da kuma tallafa wa juna.

Janar Musa ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu sojoji na sake yin wani shiri domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan al’ummomin da ke kan gaba a matsalar tsaro.

Wannan yana nuna ci-gaba da sadaukar da kai ga ɗaukar matakan tsaro da barazana yayin da mazauna da yawa suka yarda da ingantaccen tsaron.

Al’umma a Batsari sun yaba da ƙoƙarin baya-bayan nan, musamman tattaunawar da aka yi da masu laifin da suka tuba, wanda ya taimaka wajen raguwar tashin hankali.

Duk da haka, wasu sun bayyana damuwarsu. Malam Lawal Rabi’u, wani mazaunin yankin, ya nuna damuwarsa kan hare-haren ’yan bindiga daga ƙananan hukumomin da ke maƙwabtaka da su inda har yanzu ba a fara aiwatar da shirin na sulhu ba.

Duk da waɗannan ƙalubalen, babban saƙon sojoji yana ba da ƙarfi da begen yin gamayya. Kiran da Janar Musa ya yi na haɗin kai inda ya ce, “Tare, za mu iya dakatar da ci gaba da tashin hankali da muryar zaman lafiya,” ya yi ƙarfi a tsakanin waɗanda suka halarta, yana mai jaddada ra’ayin cewa dawwamammen zaman lafiya ya dogara ne da haɗin gwiwar sojoji da ’yan Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Samarin Arewa sun yaba wa Sarkin Daura kan bai wa Ja’o’ji muƙami
  • Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina  Cikin Masifar Yunwa
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’dda 1,770 sun kama 3,070 a Arewa —Janar Musa
  • ’Yan kasuwar da suka ɓoye kayan abinci na tafka asara
  • Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya
  • Manyan Bankuna 5 Da Suka Samu Ribar Naira Tiriliyan 17.3 A Nijeriya
  • Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe
  • Rashin Wutar Lantarki: Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa Na Samun Wutar Awa 2 Ne Kacal A Kullum
  • Sharhin Bayan Labarai: Shin Kissan Mutanen Gaza Gaba Daya