Aminiya:
2025-04-27@18:32:36 GMT

’Yan Boko Haram sun kashe mutum 12 a Borno

Published: 27th, April 2025 GMT

Mayakan Boko Haram sun halaka mutum goma sha biyu da jikkata karin biyu bayan wani hari da suka kai kan kauyen Bokko Ghide a Karamar Hukumar Goza ta Jihar Borno.

Wakilinmu ya ruwaito cewa cikin wadanda aka kashe akwai ’yan sa-kai biyu da wasu mutum 10 da suka fita debo itacen girki.

Sulhu da ’yan bindigar Katsina: Gaba aka ci ko baya? Abubuwan da suka faru yayin jana’izar Fafaroma Francis

Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mayakan sun yi wa ’yan sa-kan kwanton bauna a kan hanyar Kirawa da ke gudunmar Pulka.

“Sun fita neman itace ne a jeji a ranar Asabar, yayin da yaran [mayakan Boko Haram] suka yi musu kwanton bauna, inda suka kashe mutum 10 sannan wasu suka ji munanan raunuka.

“Mun binne mutum 10 sannan biyu da suka jikkata an mika su asibiti.

“Abin takaici shi ne biyu daga cikin yan sa-kai sun sadaukar da rayuwarsu wajen kare mutanenmu wadanda aka kashe ranar Juma’a.”

Bayanai sun ce harin ya auku ne yayin da ake kokarin ganin an mayar da jama’ar yankin garuruwansu don su ci gaba da rayuwa, bayan kwashe shekaru da dama suna gudun hijira a wasu wurare saboda hare-haren na ’yan Boko Haram.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram jihar Borno

এছাড়াও পড়ুন:

Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe

Wani mummunan al’amari ya girgiza al’umma a Ƙaramar Hukumar Kwami, Jihar Gombe, inda ake zargin wani magidanci ya jagoranci sacewa da kashe ɗansa mai shekara shida domin yin tsafin kuɗi.

Ana zargin cewa mahaifin yaron shi ne jagoran kisan kuma Yana cikin waɗanda suka tsere, a yayin da hukumomi ke ci gaba da farautar sa.

Tuni ’yan sanda suka cafke mutane takwas bisa zargin wannan aika-aika a unguwar Bura-Bunga da ke ƙaramar hukumar.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya sanar cewa waɗanda suka shiga hannu sun amsa cewa sun kashe yaron ne bisa umarnin bokaye da suka nemi sassan jikin ɗan Adam don yin tsafin kuɗi.

An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa 

Bincike ya nuna wani mai shekaru 45, wanda ake zargin shi ne shugaban gungun, ya hallaka yaron tare da raba sassan jikinsa gida biyu.

Ɓangaren sama na jikinsa an jefa shi cikin rijiyar, yayin da ɓangaren kasa aka bai wa abokan laifinsa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu bokaye biyu ne suka nemi sassan jikin yaron, kuma wani matashi mai shekaru 18 ne ya sace yaron, sannan wani ya haɗa bokayen da su.

Kwamishinan ’yan sanda, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa za a tabbatar an gurfanar da duk masu hannu a wannan mummunan kisa a gaban ƙuliya.

Ya kuma yi kira ga jama’a su riƙa sa ido tare da bayar da rahoto kan duk wani abu mai kama da waɗanda ake nema jami’an tsaro.

Rundunar ’yan sanda ta jaddada aniyarta na kawo ƙarshen irin waɗannan munanan laifuka a faɗin jihar ta Gombe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe sojoji 12 a barikin Nijar
  • Ƴan Fashi Sun Sace Fasinjoji 7, Ƴansanda Sun Ceto 2 A Kwara
  •  Nigeria: Boko Haram Ta Kashe Mutane 12 A Borno
  • Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno
  • Zulum Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Boko Haram Ke Dawowa Wasu Yankuna A Borno
  • Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja 
  • Janyewar sojoji ke ba Boko Haram damar ƙwace yankuna —Zulum
  • Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe
  • Zulum Ya Taya MNJTF Da Gwamnatin Alihini Bayan Harin Boko Haram A Wulgo