HausaTv:
2025-05-25@08:25:52 GMT

Falasdinawa 39 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’o’I 24

Published: 27th, April 2025 GMT

A cikin sa’o’i 24 da su ka gabata an sami shahidai 39 sanadiyyar hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamaya su ka kai a sassa mabanbanta na zirin Gaza.

A birnin Khan-Yunsu Falasdinawa 3 sun yi shahada, daga cikinsu da akwai karamin yaro, yayin da wasu da dama su ka jikkata.

Majiyar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta ambaci cewa, wani masunci ya yi shahada  saboda harin da ‘yan sahayoniya su ka kai masa a gabar ruwan garin Khan-Yunus.

A wani labarin daga yankin na Gaza, sojojin HKI suna ci gaba da rusa gidajen fararen hula a arewacin birnin Rafah dake kudancin zirin Gaza.

Tun da HKI ta sake komawa yaki gadan-gadan akan al’ummar Falasdinu a ranar 18 ga watan Maris, Falasdinawa 2,111 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 5,483 su ka jikkata.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza da ta fitar da wannan kididdigar ta kuma bayyana cewa; tun daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu jumillar Falasdinawan da su ka yi shahada, sun kai 51,495 wadanda kuma su ka jikkata sun kai 117,524.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Donal Trump Ya Kori Gomomi Daga Cikin Ma’aikata A Majalisar Tsaro Ta Kasar Amurka

Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sallami ma’aikata da dama a majalisar tsaron kasar Amuka saboda gazawarsu wajen magance wasu al-amuran tsaro da siyasa a kasar.

Tashar talabijin Ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Rauters yana cewa ma’aikatan maimakon su magance al-amuran tsaro da suka shafi tsaron kasa, sai sun zauna suna jiran abinda shugaban zai fada don su yi aiki a kansa.

Labarin ya kara da cewa shugaban ya dauki wannan matakin ne don ya mika wasu ayyukansu ga Pentagon da FBI da wasu ma’aikatun tsaro don magance wasu matsaloli masu muhimmanci a cikin sauri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kafafen Watsa Labarun Isra’ila: Kungiyoyin Kasa Da Kasu Sun Ki Shiga Cikin Shirin Isra’ila Da Amurka Na Raba Kayan Agaji
  • Rashin abinci mai gina jiki a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane 299
  • SojojinHKI Sun Kashe Akalla Mutane 75 A Gaza A Ranar Jumma’a Kadai
  • Donal Trump Ya Kori Gomomi Daga Cikin Ma’aikata A Majalisar Tsaro Ta Kasar Amurka
  • A Yemen An Yi Gangamin Miliyoyin Mutane Na Nuna Goyon Bayan Falasdinawa
  • Majiyoyin Iran Sun Musanta Da’awar Karya Kan Neman Ziyarar Amurka Zuwa Cibiyoyin Sojojinta
  • Tinubu Zai Bibiyi Kwazon Ministocinsa A Ranar 29 Ga Watan Mayu
  • Limamin Masallacin Jumma’a A Nan Tehran Ya Yi Magana Dangane Da Kwatar Garin Khurramshar Daga Sojojin Sadam
  •  Fiye Da  Falasdinawa 50 Ne Su Ka Yi Shahada A Yau Alhamis
  • Sojojin Yemen Sun Kai Wa Filin Jirgin Saman “Ben Gorion” Hari Sau Biyu A Yau Alhamis