Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata.

Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa.

A jawabinsa yayin taron, Gwamna Umar Namadi ya yi jinjina ga marubucin littafin bisa rubuta cikakken tarihi da zai amfani al’umma, musamman matasa masu tasowa.

Malam Umar Namadi ya kuma yi alkawarin umurtar ma’aikatar ilimi ta jihar da ta sayi kwafin littafin domin amfanin ɗalibai a makarantun gwamnati.

Gwamna Umar Namadi ya kuma sayi kwafi bakwai na littafin a madadin iyalinsa kan kudi naira miliyan daya, yayin da Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar ta sayi kwafi kan kudi naira miliyan biyu, sannan Sanata mai wakiltar Jigawa Arewa Gabas ya sayi littafin kan kudi naira miliyan daya.

Sauran sun hada da Kananan Hukumomin da ke karkashin Masarautar Hadejia, inda kowanne ya bayar da gudummawar naira dubu dari biyu, Shugaban Karamar Hukumar Kafin Hausa ya bayar da naira dubu dari biyar, tare da wasu hukumomin gwamnati, da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma mutane daban-daban.

An tara sama da naira miliyan bakwai a yayin kaddamar da littafin tarihin Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, a garin Kafin Hausa.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa naira miliyan Umar Namadi

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Alhazan Jihar Kaduna Ta Wajibta Gudanarda Binciken Lafiya Ga Maniyatan 2025

 

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa dukkan mahajjatan da suka yi rijista domin aikin Hajjin 2025 dole ne su gudanar da binciken lafiya cikin wannan mako.

 

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi, ya fitar, inda ya bayyana cewa aikin na da nufin tantance lafiyar mahajjata kafin tafiya wannan tafiya ta ibada. Binciken lafiyar ya haɗa da gwajin ciki na dole ga mata masu shirin zuwa Hajji.

 

Abdullahi ya bayyana cewa wannan mataki ba domin hana kowa yin Hajji ba ne, sai don tabbatar da cewa an tanadi cikakken tallafin lafiya musamman ga mahajjatan da ke fama da cututtuka kamar su ciwon sukari da hawan jini. Ya kuma ƙara da cewa za a rika ba mahajjata abinci sau biyu a rana yayin da suke a Saudiyya.

 

Ya jaddada cewa sai an yi gwaje-gwajen ne a asibitocin gwamnati da aka amince da su kafin a karɓa.

 

“Gwajin lafiya da na ciki wajibi ne. Duk wani mahajjaci da ya ƙi amsa kiran gwajin na iya rasa gurbin hajjin sa,” in ji sanarwar.

 

An kuma shawarci mahajjata da su karɓi katin lafiyarsu daga hannun jami’an rijista kafin su tafi zuwa asibitocin da aka ware domin gudanar da binciken.

 

Rel/Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Alhazan Jihar Kaduna Ta Wajibta Gudanarda Binciken Lafiya Ga Maniyatan 2025
  • Gwamna Buni Ba Zai Shiga Hadakar Jam’iyyun Adawa ba – Mai Magana Da Yawunsa
  • An Gano Naira Miliyan 27.8 Da Suke Zirarewa A Albashin Kano
  • Gwamnatin Kano Ta Gano  An Biya Wasu Ma’aikatan Bogi Naira Miliyoyi
  • ‘Yan Bindiga Na Kakaba Harajin Miliyoyin Naira Ga Mutanen Zamfara
  • Manyan Bankuna 5 Da Suka Samu Ribar Naira Tiriliyan 17.3 A Nijeriya
  • Masana’antun Nijeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 1.11 Wajen Samun Wutar Lantarki A 2024 – Rahoto
  • Jigawa Ta Bude Sabon Babi: Maniyyata Za Su San Masaukansu Tun Daga Gida Najeriya
  • Kudaden Da Ke Hannun Mutane Sun Ragu Zuwa Naira Tiriliyan 5 – Rahoto