Yadda matsalar ƙwacen waya da faɗan daba ke addabar Kano
Published: 27th, April 2025 GMT
Matsalar faɗace-faɗacen daba da kuma ƙwacen waya na ci gaba da ci wa al’umma Jihar Kano tuwo a ƙwarya, domin kuwa babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba ba ko na ƙwacen waya a sassan jihar ba, abin da ke sanya fargaba a zukatan al’umma.
Munin lamarin ya kai matakin da akwai wuraren da mutane ba sa iya zuwa da daddare saboda tsoron mummunan abin da ke iya samun su.
Wasu na ganin yadda ake gudanar da siyasar jihar da kuma yadda rashin aikin yi su ne ummulahaba’isin wannan matsalar musammam a tsakanin matasa.
Wani ma’aikacin kiwon a lafiya a sashen bayar da agajin gaggawa a daya cikin asibitiocin jihar ya ce, kusan kullum sai an kawo wadanda suka sami raunuka, sakamakon fadan daba ko a hannun masu kwacen waya.
Ya ce “Wannan ce shekarata ta biyu a wannan bangaren kuma magana ta gaskiya kullum sai an kawo masu rauni a wannan bangaren domin a kula da su.
“Na fi shekarau 19 ina wannan aiki, amma ban taba ganin abin tashin hankalin irin wannan ba, kuma idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, to tabbas akwai babbar barazana ga zaman lafiya.”
Yadda suke ta’asarMatasan da ke aikata wannan ta’asa suna amfani da fadan daba su afka wa mutane su kwace musu wayoyin hannu da kuma kudade.
Haka ne ma ya sa mutane da yawa ba sa iya fito da wayoyinsu domin amsa kira a wasu wuraren.
Wasu kuma sun kaurace wa wuraren da ayyukan bata-gari ya yi kamari.
Wani magindanci mai suna Aminu Baffa, ya ce an kwace masa wayar da bai fi sati da saya ba.
Ya ce abun ya faru ne a Kofar Mata da misalin karfe 10 na dare inda bayan ya kira mahaifiyarsa a waya, wasu matasa uku dauke da muggan makamai suka nufo shi, suka ce, ‘Gama wayar ka ba mu.’
Ya bayyana cewa mahaifiyar tasa “ta ji maganarsu, don haka ta ce kada ka ja da su, ka mika musu wayar baki alaikum.”
Daga baya wani a cikinsu ya jefa masa layin wayarsa.
Shi ko wani saurayi mazaunin unguwar Shagari Kuarters, yankan da aka yi a goshinsa yayin masu kwacen wayar suka same shi a kofar gidansu da misalin karfe 9 da dare, suka kuma kwace masa waya. Sai da aka yi masa dinki a raunin da suka ji masa.
To sai dai wani mazaunin unguwar Dorayi mai suna Awwalu Maiwada ya ce ana samun saukin ayyukan bata-gari da masu kwacen waya, saboda irin sabbin matakan da gwamnati take dauka domin tabbatar da tsaro.
A yi wa tufkar hanci tun da wuriA farkon watan Afrilu da muke ciki ne aka tsinci gawar wata matar aure ’yar shekara 23, Ruma Shu’aibu, a kwance cikin jini, a unguwar Farawa cikin Karamar Hukumar Kumbotso, lamarin da ya sa mazauna unguwar cikin dimuwa saboda sun san matar mai son maman lafiya ce.
Mijinta, Ibrahim Muhammad, wanda ya ce ya bar ta a gida, ya bayyana cewa hankalinsa ya tashi lokacin da ya kira wayarta ba ta dauka ba, don haka ya nemi makwabcinsa ya duba amma shi ma ba wanda ya amsa liransa, ko da mijin ya dawo gida, sai ya tarar da ita a kwance cikin jini kuma an dauke wayarta.
Haka nan, an guntule wa wani malamim makaranta, Aminu Umar, yatsa, yayin karbar wayarsa a kan titin zuwa Jami’ar Bayero ta Kano, abin da ke alamta irin kalubalen da ke gaban gwamnoni.
Mutane na nuna damuwa bisa yadda dadan daba a unguwaani irin su Yakasai da Sabuwar Kofa da Kofar Mata da Dorayi da Sharada da Kofar Na’isa, kan kai ga zubar da jini ko ma rasa rayuka a tsakanin matasa.
Da yawa kuma ana wucewa da su zuwa asibiti domin samun kulawa da lafiyarsu.
Dalilin ƙaruwar faɗan daba da satar waya a KanoWani tsohon jami’in dan sanda, Sami Mohammed, ya ce, “Abin da ke kawo hakan bai da wahalar.
“Matsin tattalin arziki da talauci da kuma tashin farashi sun jefa matasa cikin kunci, shi ya sa suke daukar kwace waya da harkar daba domin kaiwa tudun mun tsira.
“Abu ne a fili, mutane kusan kashi 70% ba sa yarda su fito da wayarsu bainar jama’a su buga, saboda tsoron masu kwacen waya,” in ji shi.
Ya kara da cewa “abin da yake sa lamarin ke ci gaba shi ne kasuwannin da ake sayar da wayoyin hannu na sata na ci, ta yadda barayin sun san inda za su sami mai sayen wayar cikin ’yan awanni.”
Matakan da Gwamnatin Kano ta ɗaukaA shekarar 2023, Gwamnatin Kano da rundunar ’yan sandan jihar sun dauki aniyar kawo karshen wannan matsalar, inda gwamnatin ta yafe wa wasu batagarin matasa 222 da suka tuba kuma aka dauki 50 daga cikinsu a matsayin ’yan sandan sarauniya (special constabulary).
Kazalika gwamnatin ta kafa kwamitin tsaro na musamman karkashin Kwamishina, Dokta Yusuf Kofar Mata, domin kawo karshen matsalar.
Kazalika, Mataimakiya ta Musamman ga Gwamna kan Tsaron Al’umma, Ambasada Dakta Maimuna Umar Sharif, ta ce suna wayar da kan jama’a kan harkokin tsaro tare da sama wa ’yan sanda motocin aiki, da kuma samar da fitilu masu amfani da hasken rana a kan tituna a birni a karkara.
Ta ce nan ba da daɗewa ba za a ƙaddamar da gidauniyar tsaro kamar yadda Jihar Legas ta yi domin samar da issassun kudaden gudanar da ayyukan tsaro.
Kazalika kwamishina ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Dikko, ya shirya taro da dukkan masu unguwanni da turawan ’yan sanda daban-daban domin cimma matsaya kan yadda za a fuskaci matsalar, kuma mataimakin gwanar jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ma ya samu hallartar zaman.
Yadda za magance dabanci da ƙwacen waya a KanoWani masanin harkokin tsaro, Awwalu Durumin Iya, ya zayyana hanyoyin da za a kawo karshen matsalar.
Da farko, in ji masanin, “Tilas gwamnati ta samar da hanyoyin ayyukan yi ga dimbin matasa masu zaman kashe wando a sassa da lunguna.”
A cewarsa, “samun aikin yi dai dauke hankalinsu daga yawan fadace-fadacen daba da satar waya ko kwace.”
Durumin Iya ya ba da misali da garin Kura wanda mafi yawan mazauna yankin ’yan tauri ne, amma ba a fiye samun matsalolin tsaro da fadace-fadacen daba ba, saboda mafi yawa suna aikin gona da kuma noman shinkafa.”
Masanin ya kara da cewa, “Tilas a kawo karshen jagaliyar siyasa,” wadda yake ganin ita ce matsalar da ke kara taimaka wa matasan suke yin rawar gaban hantsi a zamantakewa da kuma sha’anin siyasa.
Ya yaba wa hukumar ’yan sanda saboda aiki tare da sarakunan gargajiya wajen tattara bayanai da kuma jan kunne ga masu aikata wadancan miyagun ayyuka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faɗan Daba Jihar Kano masu kwacen waya kawo karshen ƙwacen waya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudin al’umma ba ga mutanen da ba za su iya kula da mahajjata yadda ya kamata ba.
Gwamna Radda ya kara da cewa ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi guda 34 domin tabbatar da cewa malaman da suka cancanta ne kadai aka zaba a matsayin masu koyarwa a ayyukan aikin hajjin bana.
Ya kuma yi alkawarin kafa kwamitin yada labarai domin yada ayyukan aikin hajjin tare da ba da kulawa ta musaman kan shawarwarin da aka bayar kan rahoton da kwamitin aiki hajjin ya gabatar.
Da yake gabatar da rahoton, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina kuma Amirul Hajj, Alhaji Tukur, ya bayyana wasu muhimman batutuwa da ke bukatar kulawa.
Ya kuma bayyana bukatar tallafa wa hukumar kula jin dadin alhazai wurin tantance malamai. Yana mai cewa mafi yawancin shugabannin kananan hukumomi sun sanya malaman da ba su da kwarewar yadda za su koyar da mahajjatan.
Amirul Hajja ya nuna damuwarsa bisa yadda ake samu wadanda ba ‘yan Nijeriya ba a cikin mahajjatan jihar tare da ba da shawarar inganta hanyoyin da ake bi wurin tantance mahajjatan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp