Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare
Published: 27th, April 2025 GMT
A cewarsa, kasar Sin ba ta neman kakaba akidunta kan sauran kasashe. Abun da take nema shi ne, aminci da tuntubar juna. Kuma a ganinsa, wannan shi ne ya kamata ya kasance ruhin hadin gwiwa.
Bugu da kari, ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar game da tabbatar da tsaro da zaman lafiyar duniya da ci gaban duniya da hadin gwiwa ta fuskar al’adu, sun dace da muradun MDD na wanzar da zaman lafiya da gudanar da ayyukan agaji da tabbatar da tsaro a duniya, yana mai cewa, akwai babbar dama ta kara hadin gwiwa a cikinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Zulum Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Boko Haram Ke Dawowa Wasu Yankuna A Borno
Zulum ya bayyana wasu matsaloli da ke kawo tsaiko, ciki har da ƙarancin sojoji a yankunan Timbuktu Triangle, Tumbus, tsaunin Mandara, da kan iyakar Nijeriya da ƙasashen Sahel.
Ya roƙi Ministan Tsaro da ya turo ƙarin manyan makamai da motocin yaƙi na zamani zuwa Borno domin taimaka wa sojoji.
A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura ƙarin kayan aiki da jami’an soja don magance matsalar tsaro a Borno da Arewa Maso Gabas.
Ya ce shugaban ƙasa ya umarce su da su tabbatar da samar da duk abin da ake buƙata domin murƙushe ‘yan ta’adda a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp